Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar ceto yara biyu da aka sace a yankin Tilden Fulani, Ƙaramar Hukumar Toro, tare da kama wanda ake zargi da aikata laifin — wanda daga baya aka gano cewa ‘dan uwan mahaifin yaran ne.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar Alhamis, 23 ga Oktoba, 2025, lokacin da wani mai suna Aliyu Hamisu ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Tilden Fulani cewa ‘ya’yansa biyu Halima Hamisu mai shekaru 12 da Mohammed Aliyu Hamisu mai shekaru 6 sun bace yayin da suke jiran motar makaranta a bakin titi.
Binciken farko na ‘yan sanda ya gano cewa wani mutum da ke cikin keke Napep ne ya ɗauke su.
Bayan wani lokaci, wanda ya sace yaran ya kira iyayensu inda ya nemi kudin fansa naira miliyan hamsin (₦50,000,000). Daga bisani, bayan tattaunawa, ya amince zai karɓi naira miliyan ɗaya da dubu dari biyu (₦1.2m).
Jami’an ‘yan sanda, cikin dabarar aiki, sun shirya yadda za a kama wanda ake zargi a wurin da aka tsara don bayar da kudin fansar a kusa da kwanar Farmers Motors, cikin Bauchi.
Bincike ya kai jami’an zuwa Anguwan Rukuba a birnin Jos, Jihar Filato, inda suka samu damar ceto yaran cikin koshin lafiya, sannan suka mika su ga iyayensu.
Bayan kama wanda ake zargi, an gano sunansa da Abdulkarim Tasiu, wanda ‘dan uwan mahaifin yaran ne. A lokacin bincike, ya amsa laifinsa, yana mai bayyana cewa tsohon sabani tsakaninsa da mahaifin yaran ne ya sanya shi aikata wannan mummunan laifi.

