Daga: Comrade Abbas Ibrahim
Su ne murya mai amo ta labarai —
Masu kawo mana rahoto da ra’ayoyi,
Masu Sanya shugabanni Tsayawa Kan Daidai,
Masu bayyana gaskiya ga al’umma.
Su ne ke nishaɗantarwa, ilmantarwa, da kuma zaburar da tunani.
Amma a hannu guda, ga ma’aikatan wucin-gadi,
Rayuwarsu cike da rashin tabbas,
Babu ‘yanci! Babu kariya!! Babu tabbacin gobe.
Sun makale cikin tsoron rashin albashi madaidaici.
Commissioner Visits Dorayi Babba Psychiatric Center, Shahuci
Harkokin yada labarai sun cika da jarumai —
‘Yan jarida masu kai-komo a cikin dare, suna zabarin nemo gaskiya,
Suna fassara manufofin gwamnati don jama’a su fahimta,
Suna fito da kura-kurai da ke cikin tafiyar mulki don a gyara, ba don cin zarafi ba.
Sai dai albashinsu ya gaza, a zahiri ba su da albashin ma, sai dai kudin alawus da ba shi da tabbas kuma ba ya iya biyan bukatunsu.
Suna fuskantar tsangwama,
Wasu ma suna tura kansu ga ayyukan da ba su dace ba,
Domin samun abin kai wa baka.
“Rayuwa ba wai jiran ganin ranar tsira ba ce, amma koyon yadda ake fidda kitse ne a cikin wuta.
RENO’S FACTFINDERS: Genocide Spin, Coup Whispers and Foreign PR Mercenaries
‘Yan uwansu a wasu wurare suna morewa,
Amma su, zuciyarsu ta gaza samun nutsuwa da kwanciyar hankali.
Daga cikin wadannan ma’aikata na wucin gadi, akwai masu dauko rahotanni da
masu gadi da masu aikin tsafta da direbobi da injiniyoyi da
masana fannin fasaha da masu shirye-shirye da masu gyara sauti da
masu kula da lambu da ma’aikatan ofis — duk suna taka rawa don tafiyar da kafafen yada labaran.
Shi kuwa shugaba yana tsaye yana kokarin daidaita lamura.
Sai dai, wadannan ma’aikatan wucin-gadi na kafafen labarai
Na jiran mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf,
idanun su cike da fatan alheri da
Fatan jinƙai daga zuciya mai tausayawa,
Wadda za ta kawo farin ciki a rayuwar da aka dade ana wahala.
Sun yi amanna a zukatan su cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, Mai son talakawa ne, mai kula da jama’a ne.
Kuma sun sani cewa shi farin ciki duk lokacin da ka sanya shi a zukatan wasu, yana dawowa ne da ninkinsa.
Gwamna Yusuf, zuciyarsa zinariya ce, Ya faranta ran dubban malamai ‘yan BESDA da su da iyalansu.
Ya yada farin ciki a gidaje masu tarin yawa.
Shugabanni nagari su ne masu sanya murmushi a fuskar al’ummarsu.
Duk da cewa ba su da yawa, amma ma’aikatan wucin-gadi na kafafen labarai
Su ne jaruman da ba sa samun yabon da ya dace.
Su ne zuciyar al’umma, masu bayyana gaskiya.
Rayuwar ma’aikatan wucin-gadi tana cikin hadari —
Babu murya! Babu ƙungiya!!
Allah Sarki! Wannan shi ne halin da suke ciki.
Amma kar ku yanke ƙauna —
Allah Maɗaukaki ne Mai magance duk wata damuwa.
Na gode. Ina ƙaunarku dukka.
Naku a ko da yaushe,
Comrade Abbas Ibrahim.

