Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar Tufafi ta Kantin Kwari a jihar Kano Alhaji Balarabe Tatari yayi kira ga ‘yan kasuwa da su guji fadawa hannun batagari masu tura shaidar biyan kudi a banki ta bogi. 
Alhaji Balarabe Wanda Kuma shi ne shugaban gidajen Kantin Kwari  yayi wannan Kiran ne biyo bayan korafe korafe da suka samu daga masu siyar da kaya a kasuwar. 
Ya bayyana cewa yanzu ‘yan damfara sun bijiro da wata hanya ta zamba cikin aminci inda suke siyan kaya tare da karbar lambar asusun bankin Wanda suka yi siyayya a wajen shi. 
Shugaban yace da zarar sun yi hakan sai su yi kamar sun tura kudin tare Kuma da baiwa mai kayan shaidar cire kudi ta banki wato alert a turance. 
Balarabe ya Kara da cewa babban abun tashin hankali shi ne mutanen kan yi wani abu Mai kama da siddabaru ta yadda idan mutum ya shiga manhajar bankin ta yanar gizo wato application sai yaga cewa kudin sun shiga amma a hakikanin gaskiya yawan kudin asusun nashi dake bankin ba su karuwa akan yadda suke. 
Wato ma’ana idan kana da miliyan daya aka yi siyayyar miliyan goma aka ce an turo maka kudin  idan har alert din na bogi ne balance din ka ba zai Karu ya koma naira miliyan goma Sha daya ba zai nuna miliyan daya ne kawai wanda dama sune asalin kudin dake asusun ajiyar na ka”
Ya ce hakan na nuni da cewa kudin da ake ikirarin an tura basu shiga cikin asusun ajiyar ‘yan kasuwa. 
A don haka shugaban ya ja hankali ‘yan kasuwar da su kiyaye tare da gujewa hada hadar kudin ta banki da duk mutumin da basu san shi ba domin gujewa fadawa hannun ‘yan damfara. 
Balarabe yace an kama irin wadancan batagari da dama a kasuwar ta Kantin Kwari. 
Ya Kuma yi kira ga hukumomin da abun ya shafa da su yi gaggawar hukunta duk wanda aka kama da yin zamba cikin aminci domin cigaban harkokin kasuwanci. 
Shugaban Kasuwar ta Kantin Kwari ya Kuma musanta rade radin da ake ta yadawa na cewa da yawun shi wadansu ‘yan kasuwa ke sanya tebur ko kwantena ta siyar da kaya akan hanya. 
Ba da yawu na wadancan mutane suka saka tebura da kwantena suka tare hanya ba da ban yi hakan ba yanzu ma ba zan yi ba” 
“Akwai Kuma wadansu dake zuwa wajen ‘yan kasuwa  suna karbar kudi da suna na suna cewa  wai mun tattauna akan a basu gaskiyar magana ban San anyi ba Kuma ban aiki kowa wajen wani ba” 
Balarabe Tatari ya Kara jaddada aniyar sa wajen kare martaba da dukiyoyin ‘yan kasuwar Kantin Kwari yana Mai cewa Kofar shi a bude ta ke domin karbar  duk wani korafi. 
Share.
Leave A Reply

Exit mobile version