Jamila Sulaiman Aliyu
Gidauniyar Umma Suleiman Yan’Awaki Ta
Gidauniyar Umma Suleiman Yan’Awaki (Aunty Baby) WCDF ta roki gwamnatin jihar Kano da ta tallafa mata domin ci gaba da taimakawa matasa musamman marayu da masu karamin karfi, kasancewar rashin gata na jefa su cikin halin da ba a fatan su fada.
Ta ce samun goyon bayan gwamnati zai kara karfafa ayyukan da gidauniyar ke yi wajen inganta rayuwar matasa.
A lokacin da take bibiyar shirin horas da mata da ke da bukatu na musamman kamar kurame da makafi da Gidauniyar Women and Children Dream Foundation WCDF, Hajiya Umma ta ce an koyar da su sana’o’i guda takwas da za su ba su damar dogaro da kai.
Ta kara da cewa sama da matasa mata 400 ne ta dauki nauyin koyarwa da kudin jikinta, inda ta jaddada cewa tallafin gwamnati zai ba da damar fadada shirye-shiryen zuwa dukkan kananan hukumomin Kano.
Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana jin dadinsu da wannan taimako da Aunty Baby ta kawo, inda suka ce ta zamo uwa ga marayu, duba da cewa yawancin su marayu ne.
Daya daga cikinsu, Raihanatu, ta ce sun yi alwashin ci gaba da gudanar da sana’ar da suka koya tare da fatan nan gaba su ma su koyar da wasu.
A nata bangaren, Malama Farida ta bayyana cewa daga cikin sana’o’in da suka koya sun hada da paint work, shampoo, custard powder, washing soap, conditioner, scrub da kuma market strategies.
Wakiliyar Paradigm News, Jamila Sulaiman Aliyu, ta ruwaito cewa mata da aka zabo sun fito ne daga unguwanni daban-daban na cikin birnin Kano, kuma sun hada da matasa, mata aure da zaurawa.

