Shugaban Karamar hukumar Gwarzo Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya ce a tsawon shekaru goma Sha takwas da Barde Kerarriyar Kano Alhaji Shehu Kabiru Bayero ya yi a Karamar Hukumar Gwarzo ya gudanar da aiyukan alkhairi da ba za a taba Mantawa da shi ba, na gina masallatan Juma’a da makarantun islamiyyu da Samar da ingantatcen tsaho a loko da Sakon Yankin.

KH Gwarzo Ta Kafa Kwamitin Rijiyoyin Burtsatsai Da na Kudin Shiga

Shugaban Majalisar Karamar Hukumar ta Gwarzo ya kara da cewa suna da yakinin cewa Hakimin Mai barin gado, zai ci gaba da aiwatar da aiyukan alkhairi kamar yadda ya saba a sabuwar gundumar Dorayi da zai koma

Daga nan Dakta Mani Tsoho Gwarzo ya bada tabbacin cewa kofarsa a bude take, a Koda yaushe duk abinda ya ta so a bangaren fadar sabon hakimin Musamman bangaren tsaro, lafiya da ilimi, wajen bada gudunmawarsa dan samin nasarar da ake bukata.

Deputy Gov Aminu Gwarzo Hails Governor Yusuf on 62nd Birthday

Anasa bangaren Wakilin Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na Biyu Wanda Madakin Kano Alhaji Yusuf Labahani Cigari ya wakilta ya yi kira ga Dagatai da masu unguwanni na Karamar Hukumar ta Gwarzo da su bawa sabon hakimin hadin Kai da goyan baya wajen gudanar da mulkinsa cikin nasara .

Da Yake Jawabi ,Sabon Hakimin Gwarzo Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano Alhaji Bello Abubakar Gwarzo ya baiyana Jin dadinsa bisa tarbar da al-umar Yankin suka yi masa.

 

Sarkin Dawaki Mai Tutar ya Kuma bukaci hadin Kai na Dagatai da masu unguwanni na Yankin da su ba shi hadin Kai wajen ganin an ciyar da Karamar Hukumar gaba.

AGILE Inaugurates 2nd Chance Education Center Gwarzo LGA Kano

A Jawabinsa tsohon hakimin Karamar Hukumar ta Gwarzo Barde Kerarriyar Kano Alhaji Shehu Kabiru Bayero ya bukaci hadin Kai ga al-umar da su bawa Sabon Hakimin na Gwarzo Alhaji Bello Abubakar Gwarzo hadin Kai wajen ganin ya gudanar da mulkinsa cikin nasara.

Daraktan kudi da gudanarwa na Yankin Alhaji Ubale Magaji ya gabatar da jawabin Godiya a madadin al-umar Yankin.

Sarkin Ban Ringim Hakimin Babura, da Magajin Rafin Kano, da Shugaban Karamar Hukumar Gabasawa, da Dagatai da Karamar Hukumar ta Gabasawa da tsohon Sanatan Kano ta Arewa Distinguish Bello Hayatu Gwarzo da Dagatai da ga Karamar Hukumar Shanono da sauran Yan Siyasa na daga cikin muhimman mutanen da suka halarci Taron .

 

A karshe Dagatai Ashirin da Biyu da masu unguwannin da limaman masallatan Juma’a na Yankin Sun nuna goyon bayansu ga sabon hakimin na Gwarzo Alhaji Bello Abubakar Gwarzo Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version