Duk da cewa shekarar 2024 ta fara yi wa mutane ban-kwana, har yanzu haziƙan mawaƙan Hausa suna ci gaba da fitar da waƙoƙi domin nishaɗantar da al’umma.

Tun shekaru aru-aru, Hausawa sun yi fice wajen nishaɗantar da mutane da waƙoƙi masu cike da fasaha da hikima, musamman wajen ƙwarzanta jarumai da waƙoƙin sana’a da sauransu, kafin daga bisani aka fara waƙoƙin nishaɗi na soyayya da finafinai.

Finafinan Kannywood Biyar Da Suka fi Shahara a Shekarar 2024

A shekarar 2024, mawaƙan Hausa sun bajekolin fasaharsu wajen fitar da waƙoƙi da dama da suka ciri tuta.

Sai dai idan aka ce waƙoƙin da suka fi jan hankali, ana nufin waƙoƙin da mutane suka fi magana a kai musamman a kafofin kafafen yaɗa labarai irin su Facebook da Instagram da TikTok da kafofi irin su rediyo da talabijin.

A wannan shekarar 2024, kamar kowace shekara, BBC ta rairayo wasu waƙoƙi 10 da suka fi jan hankalin mutane.

Finafinan Kannywood Biyar Da Suka fi Shahara a Shekarar 2024

Mai kishi na – Sadiq Saleh

‘Mai kishi na’ wadda matashin fasihin mawaƙi Sadiq Saleh ya rera ta ja hankalin mutane matuƙa, kasancewar ta zo a daidai lokacin da matashin yake jan zarensa a fagen waƙoƙin Hausa.

Mawaƙi Sadiq Saleh ne ya rubuta kuma ya rera waƙar tare da zabiya Fati Nijar. Sannan zuwa ranar 16 ga Disamba, waƙar ta samu sama da masu kallo miliyan 2,600,000 a YouTube daga ranar 9 ga Satumba da ya sake ta, kuma jaruma Rukky Alim ce ta hau waƙar.

Ko a ranar 17 ga Agusta da matashin ya je wani taron ɗalibai a jami’ar ABU, waƙar ya rera, kuma mahalarta taron suka riƙa amsa suna shewa suna takawa.

‘Mai kishi na’ waƙa ce ta soyayya, kuma ta ja hankalin matasa matuƙa, musamman a kafofin sadarwa da wuraren tarukan bukukuwa na Hausa, wataƙila saboda kalaman soyayya da zuba a cikin waƙar, sannan an yi kiɗa mai ɗaukar hankali da ke sa masu sauraro rausayawa.

Amshin waƙar shi ne:

Kun ga ina jin daɗin, ina jin daɗi!

Na samu muradin raina!

Tana kishina ni dai!

Tun a ranar 5 ga Satumba ya fara tsakura waƙar a Instagram, sannan a ranar 8 ga Satumba ya ce yaushe mutane suke so a sakar musu wakar sannan a12 ga Satumba ya sanar da cewa ya sake ta, inda Instagram aka danna so wato like sau 16.1k domin murnar sakinta.

Aljannata – Auta Waziri

Aljannata waƙa ce da sabon ango, Auta Waziri ya rera, inda a ciki kamar kullum ya zubo kalaman soyayya masu ratsa zuciya.

Waƙar ta ja hankali sosai, inda daga ranar 3 ga Fabrairun da ya sake ta zuwa yanza ta samu masu kallo sama da 1,675,523/

A cikin waƙar akwai inda yake cewa:

‘In dai kika bar ni sai na sha wuya

“Sai na zam kamar tsokar da babu jijiya

‘In ba da ke ba sai dai rijiya

‘Rijiyar ma mai ɗauke da ƙugiya

‘wacce za ta caki raina, ban ƙara kwana

‘Me zai sa in kwana ban gano masoyi ba’

A bidiyon waƙar, mawaƙin ne da jaruma Zahra Aliyu suka taka rawa

Sauti – Ado Gwanja

Waƙar ‘Sauti’ waƙa ce da fitaccen mawaƙi Ado Gwanja ya rera a fim ɗin ‘Gidan sarauta’ mai dogon zango na furodusa Abubakar Bashir Maishadda.

Waƙar, wadda ya sake ta a ƙarshen shekarar da ta gabata, ya saki bidiyon ne a YouTube a Janairun 2024, kuma zuwa yanzu ta samu masu kallo sama da miliyan 1,500.

Fatima mai zogale – Dauda Rarara

Ita kuma waƙar ‘Fatima mai zogale’ waƙa ce da zuwa ɗaya ta fito, ta karaɗe kafofin sadarwa, musamman na abubuan da suka biyo bayan fitowarta.

Mawaƙai Dauda Kahutu Rarara ne ya rera waƙar kan wata mai sayar da Zogale mai suna Fatima, inda waƙar ta zama sanadiyar shuhurarata.

Ya fara saka sautin wakar a YouTube a ranar 24 ga Afrilun 2024, sannan zuwa yanzu an kalla sau 1,201,153, sannan ya saka bidiyon a ranar 1 ga Mayun shekarar, kuma zuwa yanzu an kalla bidiyon sau 1,461,686.

A cikin waƙar yana cewa:

Fati Fatima fati adon gari

Kin wuce ai daƙile

Fati Fatima fati adon gari

Kin yi kamar labule

Fati Fatima fati adon gari

Sa mani in dangwale

Fati Fatima fati adon gari.

Na gode – Auta MG

Waƙar Na gode, waƙa ce da fasihin mawaƙi Auta MG ya rera, wadda ya saka a YouTube a ranar 7 ga Agustan 2024.

Zuwa yanzu ta samu masu kallo 1,014,393.

Tawan – Nazifi Asnanic da Naziru Ahmed

Tawan waƙa ce ta haɗaka da fasihan mawaƙa Nazifi Asnanic da Naziru Ahmad suka rera, kuma ta ja hankali musamman a kafofin sadarwa.

Asnanic ya ɗora waƙar a shafinsa na YouTube a ranar 26 ga Agustan 2024, kuma zuwa yanzu an saurare ta sama da 1,143,821.

Ƙwanƙwalati – Ɗanmusa

Waƙar “ƙwanƙwalati” fasihin mawaƙi Musa Muhammad wanda aka fi sani da prince ɗanmusa ya rera.

Ya ɗora sautin waƙar a shafinsa na YouTube a ranar 3 ga Yulin 2024, kuma zuwa yanzu an saurare ta sau sama 88,300.

Ga ni – Namenj

“Ga ni” ita ma waƙar soyayya ce da matashin mawaƙi Ali Namenj ya rera. Ya fara fitar da sautin waƙar ne a ranar 10 ga Afrilun 2024, inda aka saurare ta sau 90,669, sannan a ranar 20 ga Oktona ya fitar da bidiyon, wanda shi ma ya samu masu kallo 106,345 zuwa.

Sadaki – Ali Jita

Sadaki waƙa ce ta Ali Jita da ita ma take jan hankalin masu sha’awar waƙoƙin Hausa.

Ali Jita ya daɗe yana nishaɗantar da masu sha’awar waƙoƙin Hausa da zaƙin muryarsa.

BBC HAUSA

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version