Ƙungiyar Fulani makiyaya a Najeriya ta Kulen Allah (KACRAN) ta yi kira ga hukumar raya yankin arewa maso gabas da ta ci gaba da yin tsare-tsaren da take yi na ganin an inganta harkar kiwon dabbobi da kuma daɓɓaka cigaban yankin na arewa maso gabas.
KACRAN Ta Yi Kira Ga Gwamnatin Da Ta Inganta Kiwon Dabbobi
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar wanda ya samu sa hannun shugabanta, Khalil Moh’d Bello, KACRAN ta yaba wa hukumar ta NEDC bisa ƙoƙari wajen ganin an samu zaman lafiya da sake ginda al’ummomi da kuma taimakawa makiyaya, inda ya kwatanta hukumar a matsayin abin koyi.
N2.3 Billion Livestock Empowerment Initiative Launched In Kano
“Hukumar raya yankin arewa maso gabas ta kawo cigaba sosai, ciki har da ƙoƙarinta na ganin shugabancin da za a shigar da kowa-da-kowa,” in ji sanarwar ƙungiyar.
Har ila yau, KACRAN ta yaba wa haɗin gwiwar da hukumar ke yi da ƙananan hukumomi da kuma jami’an tsaro don dawo da zaman lafiya, wanda ta ce yana da matukar muhimmanci domin ɗorewar ci gaba a yankin.
Nigeria’s Livestock Industry Attracts International Attention-Jega
“Muna kuma yaba wa NEDC kan rawa da take takawa wajen kai agaji a bala’o’i da ake samu, musamman ma iftila’in ambaliya a Maiduguri da kuma ƙoƙarinta wajen sake gyara makarantu da asibitoci da hanyoyi da kuma gadoji,” in ji ƙungiyar.
BBC HAUSA