A yayin da a yau musulman duniya ke maraba lale da shigowar watan farko na sabuwar shekarar musulmci ta shekarar 1446, bayan hijirar Annabi (SAW), Mai Girma Kwamishiniyar Ma’aikatar Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano, ta shiga sahun farko wajen taya Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar shiga sabuwar shekarar da kuma yi masa fatan alkhairi.
Wani rubutaccen sako da ya fito daga ofishin ta, ya ce Hajiya Aisha na yi wa Gwamnan fatan “sabuwar shekarar musulmci ta 1446 (AH) mai cike da albarka, taimakon Allah, damina mai albarka da ma ci gaba ta kowanne fanni”.
READ ALSO: Minister Of Women Affairs Solicits Funding For African Women
Ta kara da fatan shigar sa sabuwar shekarar da kafar inda duk wani motsin sa zai kusanta shi da ci gaba da burin sa na siyasa.
A cewar ta, “a matsayin mu na musulmai wadanda muka yi imani da Allah da tasirin addu’a a rayuwa, yau din nan wata dama ce daga Allah wacce za mu yi annafani da ita wajen addu’o’in neman ci gaba da dorewar Gwamnatin Abba Kabir Yusuf da zaman lafiya a harkokin mu na gida da ofis.
Haka zalika Hajiya Aisha ta aike da makamancin wannan sakon taya murna ga Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ta ce “zakakurin shugaba ne, dan gwagwarmayar NNPP wanda ba ya gajiya wajen ganin gwamnatin talakawa ta Abba ta dore dan ci gaban Kanawa baki daya”.
A cewar ta, “a matsayin sa na shugaba mai hangen nesa wanda kowa ya sheda, abinda Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yake bukata daga wajen masu manufar alkhairi irin sa, shi ne addu’a da fatan Allah ya cika masa burin sa na shugabantar kasar nan”. Saboda haka ta bukaci musulmai a duk inda suke da su jefa wannan buri na shugaban NNPP din a addu’oin su na murnar sabuwar shekarar.
Read Alsohttps://paradigmnews.ng/kano-a-shirye-take-ta-yaki-kwalara-da-sauran-cututtuka-kncdc/
A cikin sakon nata da ya shiga hannun manema labarai a safiyar yau, Kwamishiniyar ta ci gaba da mika fatan alkhairi da murnar sabuwar shekarar ga Mai Girma Mataimakin Gwamna, Kwamarad Aminu Abdul Salam Gwarzo, da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dakta Bappa Bichi, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Mai Girma Shehu Wada Sagagi, sauran takwarorinta kwamishinoni, masu girma ‘yan majalisar jihar Kano da na tarayya, shuwagabannin jam’iyyar NNPP da Yardaddun Matan Kwankwasiyya.
Haka zalika, Hajiya Saji ta taya daukacin ma’aikatan Ma’aikatar Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman murnar sabuwar shekarar, kamar yadda ta bukaci alhazan jahar Kano wadanda suka kammala aikin hajjin su da su yi anfani da damar zubar zunuban su yayin aikin hajjin su yi wa Kano da gwamnatin Alhaji Abba addu’ar ci gaba da zaman lafiya mai dorewa.
Ta yi anfani da damar ta yau wajen shawartar mata iyayen giji dan ganin sun dau kwararan matakai wajen kare kayuwansu, ‘ya’yansu da mazajensu daga kamuwa da cututtuka masu saurin yaduwa, kamar yadda ake fama da su yanzu.
Sannan ta sake yin anfani da damar wajen mika fata da addu’ar ta ga Allah (SWT) da ya tabbatar da bukatun Gwamna Abba Kabir Yusuf da Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso.