Lubabatu I. Garba

Hukumar Dake kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ayyana kudin kujerar aikin Hajjin bana inda ta ce maniyyatan da syka fito daga bangaten kudancin kasar Nan za su biya Naira miliyam takwas da dubu dari bakwai.

Shugaban NAHCON Ya Bayyana Cigaban Da Ya Samar A Kwanaki 100

Shugaban Hukmar NAHCON Farfesa Abdullahi Sale Usman ne ya bayyana haka ta cikin wata takarda da Mataimakiyar Daraktan Hulda da Jamaa ta Hukumar Fatima Sanda Usara ta sanya wa.hannu.

NAHCON Announces 2025 Hajj Fares for Nigerian Pilgrims

Takardar ta bayyana cewa maniyyatan da suka fito daga Jihar Borno d wasu jihohin da ke makwabtaka da ita za su biya Naira miliyan takwas da dubu dari uku.

Yayin da maniyyatan da suka fito daga Arewacin kasar nan za su biya Naira Miliyan takwas da dubu dari hudu

NAHCON Announces Plan to Abolish Dollar Payments for Hajj

A cewar takardar Hukumar ta kayyade kudin kujerar hajjin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da suka hada da fadar shugaban kasa da hukumomin jin dadin alhazai na jihohi.

Nigerian Presidency Approves Airlines for 2025 Hajj Operations

Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya yi kira ga maniyyatan da su hanzarta biyan kudin kujerar kafin lokaci ya kure

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version