Shugaban Gidan Radiyon jihar Kano, Kwamared Abubakar Adamu Rano ya ce ya sami nasarorin masu tarin yawa a shekarar 2024 da ta gabata .
Na Farfado da Martabar Gidan Rediyon Kano- Kwamared Rano
Abubakar Rano ya bayyana hakan ne yayin wani taro na karshen shekara da aka shirya domin bitar nasarori da ƙalubalen da gidan Radio ya samu a Shekarar da ta gabata.
Kano Commissioner of Info Assures Human-Oriented Projects
Ya ce shugabancinsa ya cimma nasarori kusan sittin a shekarar da kare ciki har da samar da sashin yada labarai ta kafafen zamani wato New Media da samar masa da ingantattun kayan aiki da kirkiro sashin labarai da na shirye-shirye a tashar Radio Kano ta biyu wato FM tare da nada gogaggun ma’aikata don jagorantar sassan.
Kazalika shugabancin tashar ya rubanya kudin alawus na wasu daga cikin ma’aikatan wucin gadi wato ‘yan Casual tare da samar da kayan aiki daban-daban da bijiro da sabbin shirye-shirye da kuma samar da hasken lantarki mai karfin KB 31 a tashar Jogana domin inganta aiki.
Kwamared Abubakar Adamu Rano ya yi amfani da damar wajen taya murna ga wasu daga cikin ma’aikatan gidan Radiyon na Kano da su ka kammala aikin Gwamnati tare da yi musu fatan alkhairi a rayuwarsu ta gaba.l, yana mai cewa na gaba kadan zai shirya musu taron karramawa.
Haka kuma shugaban gidan rediyon na Kano ya yi albishir cewa nan bada jimawa ba wasu daga cikin ma’aikatan wucin gadi na tashar za su rabauta da samun shaidar aiki ta dundundun.
A jawabansu, wasu daga cikin ma’aikatan sun godewa shugaban bisa bijiro da manufofi da daban-daban da nufin inganta walwalar ma’aikatan tashar tare jaddada kudirin ci gaba da aiki cikin gaskiya domin tabbatar da kwarin gwiwar da ake da shi a kansu