Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta karyata rahotannin da ke cewa ta bayar da tikitin atomatik ga dukkan ‘yan majalisar tarayya da ke kan mulki a gabanin zabukan da ke tafe.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Felix Morka, ya fitar, APC ta bayyana rahoton a matsayin labarin karya, inda ta bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da shi gaba daya.
“Mun lura da wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda aka yi wa take da cewa ‘APC Ta Ba Duk ‘Yan Majalisa Tikitin Atomatik’, wanda ke yawo a kafafen sada zumunta.
“Wannan rahoto KARYA ne kuma ya kamata a yi watsi da shi baki daya domin ba ya fitowa daga jam’iyyarmu mai girma,” in ji sanarwar.
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyya da jama’a gaba daya da su yi watsi da wannan ikirari, yana mai cewa labarin ya fito ne daga tushe na son zuciya da mummunan nufi.
Har yanzu, APC ba ta fitar da wani tsarin doka ko ka’idojin da za a bi wajen zaben ‘yan takarar ta ba a zabukan da ke tafe.