Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta buƙaci majalisar dattijai ta dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wanda aka dakatar.
Da take yanke hukunci, mai shari’a Binta Nyako ta kwatanta cewa dakatar da Natasha tsawon watanni shida da aka yi, ya yi tsauri.
INEC Receives Petition to Recall Suspended Kogi Senator Natasha
Kotun ta kuma ce shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio bai yi laifi ba, lokacin da ya hana Natasha yin magana a majalisa saboda lokacin ba ta zauna kan ainihin kujerar da aka ware mata ba.
Ta kuma buƙaci Sanata Natasha ta bai wa majalisar hakuri.
A cewar kotun, tun da ƴan majalisa suna da tsawon kwanaki 181 don zama a kowane zango, dakatar da Natasha tsawon watanni da aka yi – yana kamar hana ta aiwatar da haƙƙokinta ne ga ƴan mazaɓarta na tsawon kwanaki 180.
SERAP Files Lawsuit Over Senator Natasha’s Suspension
Har ila yau, kotun ta ce majalisar dattawa tana da damar hukunta kowane ɗan majalisa da ya yi laifi, sai dai kada hukuncin ya yi tsaurin da zai hana aiwatar da ayyukan mazaɓar ɗan majalisa da aka dakatar.
Mai shari’a Nyako ta kuma kori batun da Akpabio ya gabatar cewa kotun ba ta hurumin tsauraron ƙarar.
Tun da farko, kotun ta ci Sanata Natasha tarar naira miliyan biyar saboda raina kotu, wanda ya hana ɓangarorin biyu yin magana a bainar jama’a kan batun.
Ta kuma buƙaci Natasha ta nemi afuwa a gidajen jaridu biyu da shafinta na Facebook cikin kwanaki bakwai.
A watan Maris ne majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha bayan da ta zargi shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio da cin zarafi na lalata.
BBC HAUSA