Shugaban kamfanin SKY, Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai, ya sanar da saukarsa daga mukamin Uban Gammayyar kungiyoyin ’yan kasuwa na jihar Kano, kwanaki uku kacal bayan nadin da aka masa.
Sanarwar hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda da ya sanya wa hannu da kansa, wacce mai magana da yawunsa, Kamal Yakubu Ali, ya aikewa paradigm News.
My Aim Is To Establish Sky Scrapers Production Company-CEO
A cewar SKY, wannan mukami babban nauyi ne da bai da ikon ɗauka a halin yanzu, duk da girmamawar da ke tattare da shi.
“Muna kara godiya da duk ni’imar da Allah ya yi mana da kauna da ake nuna mana dare da rana da girmamawa da ake mana,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa:
“Ina bada hakuri da fatan alheri ga Gammayar Kungiyoyin ’Yan Kasuwan Jihar Kano bisa nadin da suka yi min a matsayin Uban Kungiya, sai dai mukamin ya yi min nauyi, bazan iya daukarsa ba. Amma ina tare da su a kowane lokaci, musamman inda ake bukatar gudunmawata.”
Don’t Allow Wealth Cause Division Among you, Shettima tells Dantata Family
SKY ya kuma yi amfani da damar wajen mika ta’aziyya ga daukacin al’ummar Najeriya bisa rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda rasuwarsa ta girgiza ƙasa da al’umma baki ɗaya.
“Allahumma Salli Ala Sayyidanan Muhammad wa ala alihi. Ni Alhaji Kabiru Sani Kwangila Yakasai (SKY) ina mika ta’aziyya ga al’ummar Najeriya gaba ɗaya bisa rasuwar babanmu Alhaji Aminu Alhassan Dantata da sauran mutanen da muka rasa, Allah ya gafarta musu, amin,” in ji shi.