Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ke nuna cewa Kwamishinan Sufuri na Jihar, Alhaji Ibrahim Namadi, na da hannu a belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.
Gwamna Yusuf ya dauki matakin ne bayan jama’a Sun yi korafi sakamakon rahotannin da suka bayyana sunan Kwamishinan a cikin takardun hukuma da suka shafi sakin wanda ake zargin.
Kano Transport Commissioner Pulls Out as Surety in Drug Case
Sanarwar hakan ta fito ne a cikin wata takarda da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Don warware batun, Gwamna Yusuf ya kafa wani kwamitin bincike na musamman da Barrister Aminu Hussain, Mai ba da shawara na musamman kan harkokin shari’a da kundin tsarin mulki, ke jagoranta.
Kwamitin na da alhakin gano gaskiyar lamarin da bayar da shawarwari kan matakin da ya kamata a dauka cikin gaggawa.
Kano State House of Assembly Clears Commissioner Nominee
Mambobin kwamitin sun hada da:
Barr. Aminu Hussain – Shugaba
Barr. Hamza Haladu – Mamba
Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba
Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba
Manjo Janar Sani Muhammad (Rtd.) – Mamba
Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba
Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatariya
Gwamna Yusuf ya bayyana damuwarsa matuka kan zargin da ake yi, tare da jaddada kudirin gwamnatinsa na yaki da safarar miyagun kwayoyi da duk wani nau’i na barna a cikin al’umma. Ya sha alwashin cewa duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa, to za a dauki matakin da ya dace, ba tare da la’akari da mukaminsa ba.
“Mun kuduri aniyar tsarkake jihar nan daga miyagun kwayoyi da duk wasu munanan dabi’u da ka iya bata mana suna. Ba za mu lamunci irin wannan hali daga kowane mai rike da madafun iko ba,” in ji Gwamna Yusuf.