Rundunar ƴansandan Najeriya, reshen Abuja, babban birnin ƙasar ta cafke mutum huɗu kan zargin shirya garkuwar ƙarya don karɓar naira miliyan biyar a hannun wani dattijo wanda ƴaƴansa mata da wasu suka kitsa.
Cikin wata sanar wa da kakakin rundunar ƴansanda Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar ta ce wani Mista Innocent ne ya kai ƙarar ɓacewar ƴarsa mai shekara 16 da ta bar gida a ranar 18 ga Yulin 2025 don zuwa rubuta jarabawa a makarantar sakandare ta gwamnati da ke Karu.
Daga bisani kuma, a cewarsa, ya samu kiran waya daga wasu mutane suna neman da ya biya kuɗin fansa don su sake ta.
Bayan samun labarin ne kuma, jami’in ɗansanda mai muƙamin DPO a ofishin ƴansanda na Jikwoyi ya gaggauta ƙaddamar da bincike kan lamarin inda kuma aka bibiyar lambar wayar da aka kira mahaifin matashiyar har aka gano waɗanda suka kira na zaune a wani gida da ke yankin na Jikwoyi Phase II.
”Daga nan ne kuma ƴansanda suka je gidan inda suka gano matashiyar tare da mai ɗakin wani Mayowa Adedeji”, kamar yadda sanarwar ta yi karin haske.
SP Adeh ta kuma ce an ga mutanen biyu suna cin abinci suna kuma tattaunawa, abin da ke nuna babu wata alama ta damuwa tattare da ita.
”Binciken da aka ƙara gudanarwa kuma ya kai ga cafke babbar yar matashiyar da saurayinta”, in ji ta.
An dai gano yayar ta haɗa baki da saurayinta wajen shirya garkuwar ƙaryar da suka yi wa ƙanwarta da burin su karɓi kuɗi kimanin naira miliyan biyar daga hannun mahaifinsu.
Ƙarin binciken da aka yi ya bayyana cewa matashiyar da aka yi garkuwar da ita, tana da masaniyar abin da aka shirya kuma ta amince za ta zauna a gidan waɗanda ake zargi yayin da kuma yayarta za ta ci gaba da zama a gidan mahaifinsu inda za ta nuna ba ta da masaniyar abin da ke faruwa.
Rundunar ta ce duka mutanen huɗu da ake zargi suna hannun ƴansanda kuma sun bayyana cewa suna da hannu a lamarin.
Za dai a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike.
BBC Hausa