An garzaya da dalibai takwas na makarantar kwana a gundumar Kandhamal ta jihar Odisha dake Kasar India zuwa asibiti, bayan wasu abokan karatunsu sun zuba musu gam a idanu yayin da suke barci.
Lamarin mai ban mamaki ya faru ne a daren Juma’a a ɗakin kwanan makaranta da ke Salaguda, kusan kilomita 248 daga Bhubaneswar, babban birnin jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa, an kai yaran asibiti bayan sun kasa buɗe idanunsu, inda likitoci suka yi ƙoƙarin raba gashin idonsu da manne.
“Likitoci sun ce manne ya haifar da mummunan lahani ga idanun yaran, amma kulawar gaggawa ta hana su rasa hangen nesa gaba ɗaya,” in ji rahoton.
Hukumomi sun kafa kwamitin bincike mai zurfi game da lamarin. A halin yanzu, an dakatar da shugaban makarantar bisa zargin sakaci da aiki.
Daily Nigerian

