Safiyanu Dantala Jobawa
Kimanin littattafai dubu dari ne majalisar karamar hukumar Garun mallam za ta raba a matsayin tallafi.
Shugaban karamar hukumar, Barista Aminu Salisu Kadawa, ya bayyana hakan yayin bikin mika tallafin wanda ya gudana a sakariyar karamar hukumar.
Zakarun Musabaqar Al-Qur’ani Ta Gudauniyar Ganduje Sun Rabauta Da Kujerun Hajji
Inda ya ce “Wannan na matsayin kason farko a jaddawalin tsarin bunkasa sha’anin ilimi a yankin. Kana ya ce “Zai cigaba da irin makamancin hakan lokaci-lokaci don ganin an taimaka wa iyaye tare da daibai duba da irin yanayin da ake ciki na matsari rayuwa”
Daga bisani, ya sha alwashin ganin duk makarantar da ta yi fice akan tsarin gasa da za bijiro da shi nan gaba kadan, to zai kara tallafawa makarantar har da malamanta.
Kana ya roki malamai da su kara jajicewa akan aikinsu ba tare da kawo wani nakasu ba.
Harkokin Karatu Sun Yi Nisa A Cibiyar Sana’o’i Ta Aliko Dangote
Tun da fari, sakataren ilimin Karamar hukumar Alhaji Sabo Muhammad Chiromawa ya bayyana wannan tamkar wata yar manuniya ce da ke nuna gwamnatin jihar Kano karkashi Gwamna Engr Abba Kabir Yusif ta dawo da ruhin ilimin firamare wanda ya fada wani irin hali a baya.
A karshe ya gode wa maigirma shugaban karamar hukumar Barista Aminu S Kadawa, bisa irin hangen nesan shi akan damuwa da ilimi yaran yankin.
Da ya ke mika sakonsa shugaban hukumar ilimin Bai-Daya(SUBEB) ta jihar Kano Malam Kabir Yusuf wanda ya samu wakilcin sakatariya a hukumar Hajiya Amina Umar, ya ce “Garun mallam ita ce ta farko wajen nuna damuwarta kan sha’anin ilimin al’ummarta. Kana ya ce “Duk bukatar da ake da ita, ma’aikatarsu a shirye ta ke.
Tinubu ya bada umarnin korar ma’aikata masu digiri ‘dan Kwatano
A karshe Hajiya Amina ta mika tallafin littattafan ga wakilan makarantun faramare dana kananan makarantun sakandire da ke yankin.
Daga cikin mahalarta targets n, sun hada da daraktan wayar da kai na SUBEB Balarabe Danlami Jazuli da Hajiya Maryam Hodi sai kuma Rano Zonal Alh Sunusi Uba Ahmad da sauran al’umma da ke yankin.