Gwamnatin jihar Kano ta ce bata da wani shiri ko kuma yunkuri na hana wasu mutane yin adawa ko kalubalanyar gwamnati ba kawai dai tanaso a yi siyasa ta mutuntuka mai tsafta ba tare da cin zarafin kowa ba.
Kano Govt Bans Live Political Programs to Promote Peace
Kwamishinan yada labarai Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na kwanaki biyu da ma’aikatar yada labarai ta shiryawa masu yin amfani da kafafen sada zumunta, dan su kara tsaftace aikin su.
Waiya ya kuma ce, da yawa wasu suna yada labaran da bashi ne ba ko dan samun mabiya wanda a cewar sa hakan ba dai-dai bane.
Da yake jawabi masani a harkokin yada labarai kuma malami a tsangayar koyar da aikin Jarida na Jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Sule Ya’u Sule jan hankalin masu amfani da kafafen yada labarai ta hanyoyin sadarwar Internet ya yi da su rinka wallafa labarin da yake na hakika ba tare da kage ba.
Masana ilimin jarida da yada labarai da dama ne dai suka gabatar da makala kan muhimmancin yada labarai sahihi.