Kwamishinan Ma’aikatar Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ta Jihar Kano, Adamu Aliyu Kibiya, ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na yin aiki tare da kungiyoyin agaji domin inganta rayuwar jama’ar da ke fama da talauci da rauni a fadin jihar.
Kwamishinan ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi bakuncin tawagar Ummatee Center for the Promotion of Public Education, Accountability, and Social Safety (Ummatee-C4PASS), ƙarƙashin jagorancin Shugabanta, Malam Gazzali Ungoggo, a harabar Ma’aikatar dake Kano.
Gidauniyar Dangote Ta Kaddamar Da Rabon Abinci Na Biliyan 16
Da yake maida martani, Honourable Kibiya ya nuna godiyarsa ga tawagar Ummatee-C4PASS bisa ziyarar da suka kawo, inda ya tabbatar musu da cewa Ma’aikatar na da buƙatar haɗin gwiwa da kungiyoyin da ke da manufa irin nasu.
“Gwamnatin mu, ƙarƙashin jagorancin Gwamna mai tausayi, Injiniya Abba Kabir Yusuf, na aiki tukuru domin rage talauci da inganta rayuwar marasa ƙarfi,” in ji Kibiya. “Amma gwamnati kadai ba za ta iya ba. Muna buƙatar goyon bayan masu hannu da shuni da ƙungiyoyin farar hula kamar Ummatee-C4PASS domin cimma nasara.”
Nageriya Bata Samu Cigaban A Zo A Gani Ba A Shekaru 64-PRP
Kwamishinan ya yi alkawarin buɗe kofa ga kowace kungiya da ke da niyyar tallafawa marasa ƙarfi, yana mai cewa irin wannan haɗin gwiwar na da matuƙar muhimmanci wajen cimma cigaba mai ɗorewa a jihar.
Ya ƙare da tabbatarwa Ummatee-C4PASS cewa Ma’aikatar za ta ci gaba da maraba da duk wani ƙoƙari da zai taimaka wajen rage talauci da ciyar da al’umma gaba.
A yayin ziyarar, jagoran tawagar ta Ummatee Malam Gazzali Ungogo ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin Ummatee-C4PASS da Ma’aikatar domin ƙarfafa ilimi, tabbatar da gaskiya da adalci, da kare marasa ƙarfi.
Ya kuma bukaci a haɗa hanyoyin tallafawa masu rauni a sabon tsarin cigaban jihar Kano na shekarar 2025 (Kano State Master Development Plan 2025).