Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa ba ta da wata matsala da kowanne dan siyasa muddin zai yi adawa mai tsafta da zata taimaka wajen haskaka hanyoyin da gwamnati za ta bi don ciyar da jihar gaba.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’amuran Cikin Gida na jihar Kano, Kwamred Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da kwamitin dattawan kungiyar masu magana a gidajen Radio da ake kira Gauta Club, a wani taron da aka gudanar a Kano.
Gauta Club Backs Kano State’s Ban on Live Political Programs
Waiya ya yaba da yadda Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ke jajircewa wajen hada kan ’yan siyasa ba tare da nuna wariya ba, da kuma kokarin ciyar da jihar gaba ta hanyar siyasa mai nagarta da fahimta.
“Gwamnatinmu ba ta da matsala da adawa, matukar za ta kasance mai tsafta, ta hankali, wadda za ta kare muradun al’umma kuma ta tallafa mana wajen ganin mun inganta rayuwar jama’a,” in ji Waiya.
Info Commissioner Moves to Sanitize Kano Political Activism
A nasa jawabin, Shugaban Gauta Club, Alhaji Hamisu Dan Wawu Fagge, ya bayyana fatan cewa irin tsaftacewar siyasa da ake yi a gidajen rediyo na jihar Kano za ta zamo abar koyi ga sauran jihohin Najeriya, musamman makwabtan jihar.
Daga cikin dattawan kungiyar da aka rantsar akwai manyan ’yan ƙasa da suka shahara wajen magana da fatawa a kafafen yada labarai. Sun hada da:
Alhaji Bashir Adamu Gaya, Idris Danzago, Alhaji Isah Bello Jaa, Alhaji Ibrahim Dan Adandan, Alhaji Damina Ali Gwarzo, Alhaji Auwalu Maiturare Bichi, Kwamred Rabiu Bala, Muhammad Idris Matashin Dan Fansho, Dan Jummai Gwaska, Injiya Dayani Tarauni, Lawan Sofi Danmasanin Gaya, Hajiya Binta Sayyadi, Hajiya Habiba Dandalla, da Aminu Bichi.
Dattawan da aka rantsar sun yi alkawarin hada hannu da gwamnatin Kano wajen inganta siyasa ta gaskiya da kishin kasa.