Abba Dukawa
A yanayi irin na Najeriya, inda matsalolin tattalin arziki da tsadar rayuwa suka yi kamari, karin haraji akan man fetur zai kara wa talakawa wahala me kawai.
Sai dai masu tsara tattalin arzikin gwamnatin ba su nuna damuwa da yadda hakan zai shafi ‘yan kasa ba.
A gaskiya, shekaru biyun da suka gabata sun kasance shekaru na gwagwarmayar rayuwa ga mafi yawan ‘yan Najeriya.
Dangote Ya Sanya Sunan Tinubu a Hanyar Shiga Matatar Man Fetur
A fada a fili ba tare da boye gaskiya ba, manufofin tattalin arzikin gwamnatin Bola Tinubu na kara wa ‘yan kasa radadi. Cire tallafin man fetur da barin darajar Naira tana yawo da kanta sun haddasa tsananin talauci; miliyoyin iyalai na rasa abinci.
Tun daga ranar da Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur a ranar hawansa mulki (29 ga Mayu, 2023), tare da faduwar darajar Naira, ‘yan Najeriya suke fuskanci hauhawar farashi da ba ta da iyaka.
A cikin wani rahoto da Financial Times ta fitar a ranar 16 ga Yuli, 2024, ta bayyana manufofin Tinubu da cewa “ba su da daidaito” kuma “idan ba a gyara ba, wannan tsarin wahalar da kai don samun sauki (shock therapy) zai ci tura.”
Matatar Dangote Tayi Karin Kudin Man Fetur
Dalilin da yasa Harajin Karin Man Fetur na Kashi 5% zai Kara Wahala:
Al’umma har yanzu na cikin halin tsananin tsadar rayuwa, rashin tabbas na tattalin arziki da wahala.
Saboda haka, kudurin gwamnatin na kara harajin kashi 5% akan man fetur da dizel, wanda za a fara aiwatarwa daga 1 ga Janairu, 2026, karkashin sabon dokar haraji, ba dai-dai ba ne kuma zalunci ne kai tsaye.
Farashin abinci da sufuri Zai hauhawa matuka, haka kuma komai daga magani, kudin makaranta, layukan waya, har zuwa wutar lantarki. Ga jama’ar da ke cikin kunci, karin farashin man fetur da dizel tamkar yayyafa gishiri ne a kan rauni.
A karkashin tsarin Tinubu, Naira ta rasa sama da kashi 60% na darajarta idan aka kwatanta da Dala. A ranar 31 ga Yuli, 2025, farashin lita daya na fetur ya kai N900, idan aka kwatanta da N187 kafin Tinubu ya hau mulki.
Wannan sabon haraji zai ci gaba da raunana kasafin kudin iyalai, wanda tuni ya ruguje saboda tsadar man fetur da ke tasiri har kan farashin abubuwan bukata a gidajen Yan Kasa kamar shinkafa da kudin motar haya.
Gwamnati na cewa wannan karin haraji zai taimaka wajen kara kudaden shiga daga bangaren da ba na man fetur ba da kuma dorewar tattalin arziki, amma hakan ba shi da tasiri idan aka duba yadda wannan mataki zai shafi iyalai, kananan ‘yan kasuwa, da ma’aikata.
Daga dukkan alamu, gwamnatin Tinubu na nuna halin ko-in-kula da halin da mutane ke ciki – abin da ya kusa kama da rashin adalci.Gwamnati na ikirarin cewa tana ajiye $600 miliyan duk wata, kuma an kara kaso 40% a rabon kudade ga jihohi tun bayan cire tallafin fetur.
To me ya sa ake kara wa ‘yan kasa haraji? Wannan sabanin manufar gyaran haraji ne da aka yi domin rage yawan haraji daban-daban.
Duk da cewa gwamnatin na sa ran samun N796 biliyan daga wannan karin haraji, hakan na faruwa ne da radadin masu amfani da fetur da tuni ke fama da hauhawar farashi, karancin abinci da tsadar sufuri.
Hujojin cewa wannan haraji zai taimaka wajen dorewar tattalin arziki ba su da karfi, musamman ganin cewa sauye-sauyen haraji da aka yi kwanan nan an yi su ne don kara yawan masu biyan haraji da dakile asarar kudaden shiga.
A yayin da ake aiwatar da gyaran haraji, babu dalilin tunin rai ko na aikatawa da zai sa a kakaba sabon haraji kai-tsaye akan man da ake amfani da shi wajen sufuri.
Gwamnatin da ke cewa “Sabon Fata” (Renewed Hope) ita ce manufarta, to wannan sabon haraji ya saba da alkawarin da ta dauka. Wannan harajin kuwa, cin amanar wannan alkawari ne kai tsaye.
Idan gwamnati na son samun karin kudaden shiga daga bangaren man fetur, ya kamata ta saurari kiraye-kirayen da ke neman a rika bin diddigin kudade, a tilasta da’a a fannin kudi, tare da dakile kwaranyar kudade a kamfanin NNPC da sauran hukumomin da ke samar da kudaden shiga.
Haka kuma, ya kamata ta kara yawan fitar da danyen mai da sayar da matatun da suka lalace.
Gwamnatin “Sabon Fata” ya kamata ta zuba jari don fadada tattalin arzikin kasa domin karfafa fannonin kasuwanci da bunkasa ribar su. Ba daidai ba ne a dora nauyi a kan talakawa a sunan gyara.
Saboda haka, gwamnatin ya kamata ta sake nazarin wannan haraji na kashi 5% akan man fetur, kuma a cire shi gaba daya daga dokar haraji.
Jama’a sun riga sun nuna damuwa da cewa karin haraji akan man fetur zai kara tsadar rayiwu da kayayyaki – lamarin da zai kara tsananta halin da mutane ke ciki.
Tuni wannan “Sabon Fata” ya koma “Sabon Fushi” domin miliyoyin mutane na fafutukar tsira da rayuwa. Ko albashin N70,000 da gwamnati ke biyan ma’aikata ba ya wadatar da su wajen sayen abubuwan bukata na yau da kullum.
Dukawa ya rubuto daga Abuja kuma ana iya samunsa ta: abbahydukawa@gmail.com