Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na ofishin Kiru ƙarƙashin Kano Strategic Command sun kama wani matashi mai suna Umar Adamu Umar, mai shekaru 27 daga karamar hukumar Fagge, Jihar Kano.
An cafke Umar ne a ranar 6 ga Agusta, 2025 a hanyar Zariya–Kano yayin da yake jigilar kilo 9 na wiwi (Cannabis Sativa, wato Colorado) da aka nannade a cikin kwanduna 19 daga Legas zuwa Kano.
Kazaure NDLEA Holds Road Show to Combat Drug Abuse Illicit, Trafficking
Rahoton NDLEA ya bayyana cewa kayan da aka kama suna da darajar kasuwa fiye da naira miliyan 10, abin da ya zama babban cikas ga hanyar sadarwar masu safarar miyagun kwayoyi.
Wannan samame ya hana ‘yan kasuwar kwayoyi samun riba mai yawa, ya tarwatsa hanyar safara da rabonsu, tare da rage kudaden da suke amfani da su wajen gudanar da sauran ayyukan laifi.
Wanda ake zargin, wanda aka dade ana sa ido a kansa, ya amsa cewa yana cikin harkar safarar miyagun kwayoyi.
NDLEA Cracks Syndicate Using Hajj Pilgrims as Cocaine Mules
Kwamandan yankin Kiru ƙarƙashin jagorancin ACGN A.I. Ahmad ya jaddada cewa hukumar NDLEA za ta ci gaba da ƙarfafa sintiri da kuma amfani da bayanan leƙen asiri domin dakile safarar miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa miyagun kwayoyi ba sa samun shiga Kano da sauran sassan ƙasar nan.