Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, karkashin jagorancin Kwamishina Dahir M. Hashim, ta ɗauki wani mataki na ci gaba wajen karfafawa al’umma da kuma farfado da muhalli.
A ranar 9 ga Satumba, 2025, a Dawakin Tofa, ma’aikatar ta raba jimillar bishiyar mangwaro guda 3,000 masu yalwar ƴaƴa ga matan karkara
A wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, an ƙaddamar da shirin ne karkashin jagorancin Anas Ibrahim Danmaliki, shugaban ƙaramar hukumar Dawakin-Tofa.
Ma’aikatar ta ce an ƙaddamar da wannan shiri ne domin inganta lafiyar abinci a cikin gida, ƙara samun kudin shiga ga iyali, da kuma ƙarfafa juriya ga sauyin yanayi, tare da bayar da gudunmawa wajen farfado da muhalli a duk fadin jihar.
Ma’aikata ta ce za cimma muradun shirin ta hanyar baiwa mata kayan da za su iya ci gaba da amfani da su, inda ta ƙara tabbatar da alkawuranta na gina al’ummomi masu lafiya da kuma samar da jihar Kano mai cike da koren ganyaye.
Ta ce matan da su ka amfana da shirin sun nuna farin cikinsu da murna tare da alkawarin amfana da shirin ta hanyar da ya dace.
Daily Nigerian Hausa

