Cibiyar inganta harkokin siye bayar da kwangila, muhalli da zamantakewa mai dorewa (SPESSECE) ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) Zariya, ta shirya wani taron horar da jami’an saye da sayarwa a fadin ma’aikatu, dake Arewacin Najeriya.
An tsara horon ne don sanar da mahalarta horon dabarun zamani a harkokin siye da Kuma bayar da kwangila.
Nigeria’s Procurement Future: SPESSECE Training Sets the Pace
Da yake jawabi yayin rufe taron, shugaban shirin, SPESSECE ABU Zaria, Dokta Abdullahi Muhammad, ya ce shirin zai magance tabarbarewar ababen more rayuwa da kuma tsarin da ake samu a harkar sayo kayayyaki a Najeriya.
A cewarsa, hakan zai toshe matsalolin da ake fuskanta yayin sayen kayan Gwamnati domin tabbatarda gaskiya.

Dokta Muhammad ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar bankin duniya sun kashe makudan kudade wajen inganta hanyoyin sayo kayayyaki na zamani, inda ya jaddada bukatar mahalarta taron su yi amfani da ilimin da suka samu ta hanyar data dace.
Ya kara da cewa “Kashi na farko na shirye-shiryen SPESSECE kyauta ne, amma bayan watan Yuni 2026, komai na iya faruwa.
Procurement Compliance Tops Agenda in New FME Projects
Don haka ina kira ga mahalarta da su yi amfani da horon Muhalli da zamantakewa mai zuwa wanda aka shirya a watan Disamba 2025,” .
Shima da nasa jawabin, babban daraktan Ecobalance Academy, Dakta Haruna Mani, ya bayyana fatansa cewa hadin gwiwar za ta haifar da kyakkyawan sakamako Mai dorewa.
Ya bayyana shirin Kano a matsayin horo na farko na ci gaba a karkashin shirin SPESSECE.
Wasu daga cikin mahalarta taron da suka hada da Saminu Sani daga Federal Polytechnic Daura da Hamisu Lawan daga hukumar kula da makarantun kimiyya da fasaha ta Kano, sun yaba da shirin, inda suka bayyana horon a matsayin wanda ya dace kuma ya yi tasiri.
Sun yi alƙawarin yin amfani da ilimin da aka samu a aikace don haɓaka ƙa’idodin sayayya.
Horon mai taken Executive Short Courses in Procurement Management, Sustainable Environmental Studies, and Social Development Studies a turance, SPESSECE ABU Zaria tare da hadin gwiwar Ecobalance Academy dake Kano ne suka shirya shi.

