Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din ministan kere-kere, kimiyya da fasaha Geoffrey Uche Nnaji, biyo bayan wasu zarge-zarge da ake masa.
Kano:Kwamitin Binciken Kadarori a Garin Ungogo Ya Mika Rahoto
Tinubu ya nada Nnaji a watan Agusta 2023. Ya yi murabus ne a yau a wata wasika inda ya gode wa shugaban kasar da ya ba shi damar yi wa Najeriya hidima. Nnaji ya ce abokan hamayyar siyasa sun yi masa zagon kasa.
Shugaba Tinubu Ya Amince da Murabus ɗin Ministan Kimiyya Nnaji
Shugaba Tinubu ya gode masa bisa hidimar da ya yi masa, ya kuma yi masa fatan alheri a ayyukan da ya yi a nan gaba.

