Safiyanu Dantala Jobawa
An bukaci iyayen yara musamman na ‘yan mata masu shekaru tara (9) da su ba da cikakken hadin kai domin tabbatar da ingantaccen gudanar da rigakafin cutar sankarar mahaifa (HPV) a jihar Kano.
An yi wannan kira ne a wani shiri na wayar da kan jama’a kan rigakafin HPV da aka gudanar a ranar Laraba a makarantar firamare ta Garun Mallam Kudu Special, da ke karamar hukumar Garun Mallam.
HPV Vaccine Community Outreach Records Encouraging Turnout in Kano
Shirin ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Aisha Ibrahim Abdulkadir, wacce ta wakilci ƙungiyar E-Health Africa, mai jagorantar gangamin wayar da kai da kuma rigakafin.
A jawabinta, ta jaddada cewa rigakafin HPV hanya ce mafi inganci da ake da ita wajen kare ‘yan mata daga cutar sankarar mahaifa a nan gaba.
Ta yi kira ga iyaye da masu kula da yara su goyi bayan shirin domin kare lafiyar ‘ya’yansu, tare da tabbatar da cewa suna zuwa da katin rigakafin ranar da za a yi musu allurar, domin samun sahihiyar takaddun shaida.
Wakilin Paradigm News Safiyanu Dantala Jobawa, ya ruwaito cewa jami’an Hukumar Ilimi ta Karamar Hukumar Garun Mallam (LGEA) sun halarci taron don nuna goyon bayansu.
Daga cikin wakilan akwai Malam Junaidu Muhammad Chiromwa, Malam Jibril Haruna, da Abdullahi Gambo, wadanda kasancewar su wajen taron ya nuna muhimmancin hadin gwiwa wajen inganta lafiya da wayar da kai a tsakanin yara.
Pathfinder Organizes townhall meeting with WDCs on HPV vaccine
A ƙarshe, daliban makarantar sun bayyana farin cikinsu da yadda aka yi musu bayani, tare da fatan cin moriyar rigakafin da za a yi musu.

