An bayyana ziyarar aiki da Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kawo Kasuwar Dambatta da kuma Karar Dabbobi da cewar wata hanya ce ta inganta tattalin Arzikin Karamar Hukumar ta Dambatta da Jihar Kano tare da inganta muhalli.

Wani kwararren masanin Muhalli Comrade Sunusi Usman Dankoro ne ya bayyana haka yayin wata hira da ‘ Yan Jaridu a jiya.

Comrade Sunusi Dankoro yace tabbas wannan ziyarar ta Gwamna Abba Kabir Yusuf ta zo a dai-dai lokacin da wannan kasuwa ta ke bukatar gyare gyare yana mai karin haske da cewar Al’ummar Karamar Hukumar Dambatta na cike da farin ciki da wannan ziyarar tare da yin godiya ga Gwamnan akan wannan yunkuri na inganta rayuwar Al’ummar Dambatta tare da farfado da tattalin Arzikin yankin.

Haka kuma Dankoro ya jinjinawa Sarkin Ban Kano, Hakimin Dambatta Alh Dr Mansur Muktar Adnan wanda ya bayyana da cewar wannan kokarin Aikin ya samu ne da gudunmawarsa a matsayinsa na jigo a Bankin Musulunci na Duniya wanda sune su ka hada hannu da Gwamnatin Jihar Kano domin gudanar da wadannan managartan ayyukan na biliyoyin kudi a wannan kasuwa mai matukar tarihi a Arewacin Jihar Kano.

Kazalika ya yabawa Shugaban Karamar Hukumar Dambatta  Ado Muhd Dambatta bisa kokarinsa na gyaran ita wannan kasuwa da ya fara yi wanda ya sa gwamnatin Jihar ta dora domin ceto Yan Kasuwar da kuma kasuwanci baki daya

Ita dai wannan kasuwa tana ci a kowace lahadi a sati sannan kuma Yan Kasuwa na zuwa daga ciki da wajen Kasar nan domin hada hadar kasuwanci musamman na Dabbobi da sauran kayan abinci da makamantansu,wanda gyarata zai kasance hanyar inganta kasuwanci da zamantakewar Al’umma a Jihar nan.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version