Wadansu batagari da ba a San ko su waye ba sun yashe asusun ajiyar bankin wani dattijo Mai shekaru sama da hamsin da biyar mai sana’ar fasassun robobi da ledoji a Kasuwar ‘YanKaba a jihar Kano.
Lamarin ya afku ne a yau Talata inda mutumin mai Suna Alhaji Ibrahim Adamu ya Ziyarci daya daga cikin manyan bankunan dake titin Murtala Muhammad a Kwaryar birnin Kano domin cire kudi.
Gwamnan Jihar Rivers Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2025
A cewar shi, tun da fari ya cire naira Dubu Dari in da ya sake yunkurin cire naira dubu ashirin Sai kudin suka ki fita, Sai ya sake yunkurin goge katin nashi Sai wani mutum dake tsaye a gefen shi Yace “ Baba kawo in goge maka Katin ka sake gwadawa”.
KNHA Urges Ministry of Finance To Print Out LGAs Statements
Alhaji Adamu ya kara da cewa Jim kadan bayan ya bar wajen cire kudin kawai Sai ya ga sakon Kar ta kwana Wanda ke nuni da cewa an cire naira Dubu dari biyar a asusun na shi .
Wanda hakan ta sa ya bazama izuwa bankin da asusun na shi yake domin ya shigar da korafi.
Ya Kuma bayyana cewa a yanzu haka wadancan batagari Sun samu nasarar kwashe kudi naira Dari bakwai da saba’in da bakwai.
Adamu ya ce,wancan mutum daya karbi Katin cire kudi domin ya goge mishi ne ya sauya mishi da wani Wanda ba na shi ba.
“Ban Kuma gane cewa ya sauya mun katin na ATM ba sai da na je bankin suka karba suka duba a computer inda suka sanar da ni cewa katin ba nawa bane, kuma a bankin ne ma aka gani cewa an Kuna cire naira Dubu Dari biyu da Kuma naira Dubu saba’in bayan an Fara cire naira Dubu Dari biyar”
“Da na sanar da bankin sun yi gaggawar toshe asusun tare da aikewa babban ofishin su korafin domin daukan matakin daya dace”
Alhaji Adamu yayi kira ga Alumma da su gujewa fadawa hannun batagari tare da kiyaye Baiwa duk wani Wanda ba su sani ba katin cirar kudi da sunan zai taimaka musu.
“Duk Kuma Wanda yayi kokarin karbar Karin cire kudi a hannun ka Kada ka bashi saboda cutar da Kai zai yi kamar yanda ka yi mun”
Idan zaku iya tunawa a makonnin da suka gabata ne Jarumar finafinan hausa Mansirah Isah ta bayyana yanda aka wawashe Mata miliyoyin nairori a asusun ajiyar ta na banki.