Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu kan dokar da za ta bada damar kirkiro rundunar tsaro ta jiha.
Hakazalika gwamnan ya sanya hannu a wasu sabbin dokoki guda biyu bayan amincewa da su da Majalisar Dokokin Jihar ta yi.
Governor Yusuf Signs Three New Laws to Boost Development
Sabbin dokokin da aka kafa su ne:
1. Dokar Gyaran Hukumar Kula da Sufuri a Birnin Kano, 2025
2. Dokar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano, 2025
3. Dokar Kafa Rundunar Tsaro ta Jihar Kano, 2025
New Year : Governor Yusuf’s 2025 Vision for Kano State
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an bayyana cewa Gwamna Yusuf ya sanya hannu kan dokokin ne a lokacin taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano karo na 25, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnati.
Da yake jawabi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatinsa na samar da ribar dimokuradiyya da kuma hanzarta ci gaban tattalin arziki da walwalar al’umma a jihar.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin tsarawa da aiwatar da manufofi da shirye-shirye da za su inganta rayuwar al’ummar Kano.
Breaking: Gov Yusuf Signs 2025 Appropriation Bill Into Law
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga goyon baya da hadin kan jama’a, yana mai bukatar su ci gaba da bayar da gudunmawa domin cimma manufofin gwamnatinsa.