Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta samu nasarar kama wani matashi da yake Sana’ar kawalcin mata masu neman jinsi, da Kuma karuwanci.
Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan inda yace jami’an su na Operation Kau da badala, ne suka kama mutunin bayan samun bayanai.
Yace wanda aka kama din yana yin amfani da dandalin manhajar kafar sada zumunta ta Whatsapp inda yake umartar mata su tura masa tsiraicin su, shi kuma yana turawa masu sha’awar irin wannan harka don ya hadasu suyi fasikanci.
Akan haka ne, rundunar Hisbah take jan hankalin al’umma musamman iyaye dasu tashi tsaye wajen kula da wayoyin yayan su, don sanin wane irin group-group, suke shiga, da Kuma sanin da wane kalar mutane suke mu’amala, yana mai cewa mafi yawancin group din da matasa ke shiga a dandalin sada zumunta na harkokin bata tarbiyyar al’umma ne.
Daily News 24 Hausa