A kokarin sa na tabbatar da ana bin dokoki sau da kafa, Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano KSCB Abba El-mustapha ya kafa wani kwamiti na musamman wanda zai sanya idanu  akan  yanda gidajen wasanni a Kano suka gudanar da shagul-gulan bikin karamar sallah.

Abba El-mustapha na wannan jawabin a yau yayin kaddamar da shugabancin kwamitin tare da membobin su karkashin jagoranci daraktan kudi da mulki na Hukumar Alhaji Abdulkarim Badamasi sai daraktan dake lura da sashin shirya fina-finai Idiris zakari ya’u zaura da kuma daraktan dake lura da sashin Dab’i  Abubakar Zakari Garin babba sai masu aikawa gwamna rahoto Namusamman daya shafi Hukumar wato (SSR da SR) da kuma sauran ma’aikatan Hukumar a matsayin membobin kwamitin.

READ MORE: Kano Censorship Board Seeks NBC Support to Curb Unlicensed Media Content

Ya ce manufar kafa wannan kwamitin shine tabbatar da bin doka tare da dakile duk wani abu da ake tunanin zaici karo da al’adah ko tarbiyar addinin musulunci.

Abba El-mustapha yace aikin kwamitin shine zagayawa gidajen wasannin domin lura da su tare da kawowa Hukumar rahoto kan yadda suka gudanar da shagul-gulan bikin sallar, a inda ya kuma yi kira ga wanda aka zabo a matsayin yan kwamitin dasu maida hankali a kan aikin da aka basu tare da kawo rahoton da ake da bukata.

Shugaban ya sha alwashin hukunta duk wani gidan wasan da aka samu da laifin karya doka Wanda hukuncin ka iya kaiwa da kwace lasisin sa na dun-dun.

READ ALSO::Hisbah Moves To Regulate Social Media In Kano

A karshe ya kuma yi kira ga masu gidajen wasannin dake fadin jahar Kano musamman masu gidajen gala da sauran gidajen kallon dake gudanar da wasa a lokacin bikin sallah dasu bi dokar hukumar sau da kafa kamar yadda suka saba yi a baya.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version