A cikin kasa da wata daya a shugabancin Jami’ar Bayero, Kano (BUK), sabon Mataimakin Shugaban Jami’a, Farfesa Haruna Musa, ya kafa sabon salo ta hanyar kaddamar da daya daga cikin manyan ayyukan walwalar ma’aikata a tarihin jami’ar – gina gidaje 500 ga ma’aikata.
Wannan mataki mai karfi an tsara shi ne domin magance matsalar karancin gidaje da ta dade tana addabar al’ummar jami’ar.
Farfesa Musa ya bayyana hakan ne a yayin Tattaunawar Registry Roundtable ta biyu da aka gudanar a zauren Majalisar Jami’ar a makon da ya gabata, inda ya bayyana wasu daga cikin muhimman abubuwan da aka riga aka cimma tun bayan hawansa ofis.
Ya kara da cewa hukumar gudanarwar jami’ar ta kai matakin ci gaba wajen tattaunawa da Babban Bankin Lamunin Gidaje na Najeriya (FMBN) domin aiwatar da aikin, tare da karin bayani cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna nan bada jimawa ba domin tabbatar da wannan shiri.

