Biyo bayan shawarwarin da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya bayar kan yadda al’ummar jihar Kano za su yi ta’ammali da ruwan sama, Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Jihar Kano (KNCDC) ita ma ta bayar da shawarwarin yadda mutane za su kare kansu daga kamuwa da cutar ta kwalara.

Darakta Janar na Cibiyar, Farfesa Muhammad Abbas ya ja hankalin al’ummar jihar Kano da kada su ɗauki lamarin cutar kwalara da wasa, saboda mummunan abin da take tattare da shi ga al’umma.

RELATED: KNHA Passes Kano State Centre For Disease Control Bill 2024

A wata sanarwar manema labarai da ta fito daga Sashin Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta hakaito Farfesa Abbas yana cewa kwalara ta kasance abar sanya firgici a jihohi da yawa na wannan ƙasa, don haka, duk da cewa har yanzu babu cutar a jihar Kano, ana kira da babbar murya ga jama’ar jihar da su ɗauki matakan kuɓutar da jihar daga wannan mummunar cuta.

Darakta Janar ɗin ya bayyana cewa sanannun alamun kamuwa da cutar sun haɗa da gudawa, da amai da kuma saurin ƙarewar ruwa a jikin mutum, yana mai bayar da shawarar cewa duk wanda aka ga yana ɗauke da ɗaya ko dukkan alamomin a hanzarta kai shi asibiti mafi kusa.

Farfesa Abbas ya jaddada cewa wajibi mutane su ɗauki matakan gaggawa na hana ɓarkewar kwalara a jihar nan ta hanyar yawaita wanke hannu da ruwa da sabulu, da shan ruwa mai tsafta, da nesantar gurɓatattun hanyoyin samun ruwa da suka haɗa ruwan sama mara kyau.

Sauran, in ji shi, sun haɗa da gujewa haɗuwa da wanda ya nuna alamar yana ɗauke da cutar, da ajiye abinci yadda ya dace da kuma wanke hannaye kafin da bayan fitowa daga banɗaki.

Darakta Janar ɗin ya kuma jaddada cewa mutane su rinƙa kasancewa a cikin tsafta a wani mataki na ƙara ɗaukar matakan kariya daga kwalara, tare da yin amfani da banɗaki yadda ya kamata, da zubar da shara a inda ya dace, da kuma wanke da ruwa da sabulu hannu kafin da bayan an ci abinci.

Ya ce, lallai a dafa abinci ya dahu sosai sannan a ajiye shi yadda ya kamata, a guji ɗanye da dafaffen naman ruwa, sannan a tabbatar an wanke kayan lambu da na marmari da ruwa mai tsafta kafin a yi amfani da su.

Ya tabbatar wa al’ummar Kano da cewa cibiyar tasa tana ta ƙoƙarin, bisa cikakken goyon bayan da yake samu da ma’aikatar lafiya, wajen mayar da hankali kan duk wata cuta da za ta haifar da matsala ga zamantakewa da walwalar mutanen Kano.

“Ina amfani da wannan damar wajen taya Gwamnan lafiya, Alhaji Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara ɗaya a karagar mulki. Haƙiƙa, salon mulkinka, yana sanya mana karsashi, sannan kulawar da ka bai wa sashin lafiya tana da ƙayarwa ainun.

“Ina kuma miƙa godiyata ga Kwamishinan Lafiya, Dakta Abubakar Labaran Yusuf saboda jajircewarsa wajen ganin an cika ƙudurorin da mai girma Gwamna yake da su a ɓangaren lafiya, da kuma sanya mu, mu shugabannin hukumomin lafiya, a hanya da yake yi”, Farfesa Abbas ya ƙarƙare.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version