Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ya yanke shawarar kin cewa komai game da rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar a jihar Kano.

Kwankwaso, da manema labarai suka tambaye shi a gidansa na Miller road da ke Kano da yammacin ranar Talata, ya ce ba shi da wani abin cewa a kan lamarin.

“Don Allah Bana son yin magana akan wannan batun . Kar ka sa ni cikin abin da bai kamata a na shiga ba. Shugaban jam’iyyar ya yi magana kuma yana magana, ku je gare shi,” Kwankwaso ya fadawa manema labarai.

Idan za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito jam’iyyar NNPP ta dakatar da sakataren gwamnatin jihar Kano, Dakta Abdullahi Baffa Bichi, da kwamishinan sufuri, Muhammad Diggol daga jam’iyyar.

A cewar Dungurawa, dakatarwar ta biyo bayan korafe-korafensu da ake kaiwa shugabannin mazabunisu da na kananan hukumomi na jam’iyyar.

Dungurawa ya ce an dakatar da su ne saboda rashin mutunta jam’iyyar da shugabancinta.

Idan za a iya tunawa a yan Kwanakin nan ana ta zargin Sakataren gwamnatin Kano Dr. Baffa Bichi bisa daukar nauyin wata kungiya mai suna “ Abba tsaya da kararka” wacce take rajin ganin an sami farraku tsakanin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Rabi’u Musa Kwankwaso.

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version