Hukumar Tsara Birane ta jihar Kano KNUPDA ta kaddamar da kwamitin da zai fara karbar koken-koken masu korafi dangane da mallakar filaye da gidaje da gonaki har ma da shaguna a fadin Jihar nan

Shugaban Hukumar Akitec Ibrahim Yakubu Adamu ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin mai mutane biyar karkashin jagorancin Daraktan Mulki na Hukumar Alh Aminu Umar.

Shugaban Hukumar yace sun lura da cewa abokan huldarsu na kokawa dangane da yadda wasu daga cikin Jami’an hukumar ke amfani da damar da suke da ita tare da yin-sama-da-fadi da sunan hukumar inda su ke aikata ba dai dai ba

Yace kwamitin zai dinga karbar korafe-korafen al’umma a ranakun Litinin zuwa Juma’a, kuma duk wanda aka samu da laifi zai girbi abinda ya shuka bisa tanade tanaden doka.

Da ya ke Jawabi, shugaban kwamitin Alhaji Aminu Umar yasha alwashin yin aiki tukuru don magance matsalar da hukumar ke fuskanta, yana mai karin haske da cewar zasu dauki mataki nan take ga duk wadanda suka samu da laifi, tare da gabatarwa Hukumar kundin korafe-korafen da suka karba duk bayan watani shida.

‘Yan kwamitin sun hadar da Aminu Umar a matsayin Shugaba, da Mujtaba Inuwa da Kabiru Musa Dagumawa da Sani Salisu Kabara sai Abubakar Bala a matsayin magatakardar kwamitin.

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version