AISHA ADAM GIMBIYA

Ranar 25 ga watan Nuwabar kowace Shekara ce majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar gangamin yaki da cin zarafin mata da ‘ya’ya mata ta duniya.

Ranar an ware ta ne domin wayar da kan al’umma muhimmancin kare ‘ya’ya mata daga cin zarafin su da kuma daukar matakan da suka dace, Taken ranar ta bana shi ne “Hangen nesa dangane da Mata a nan gaba”.

Put Your Pasts Behind, Embrace Resilience, Minister To GBV Survivors

To a wannan makon ne aka yi makon kare mata daga cin zarafin su, wakiliyar mu ta tattauna da wasu mata kan irin cin zarafin da suka fuskanta.

Malama Ladidi daga karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna ta bayyana yadda kishiyar mahaifiyar ta hana ta karatu ta mata auren dole.

Ita kuwa Malama Jummai daga karamar hukumar Kagarko bayyana yadda talla ya lalata mata rayu ne har ta dauko abin kunya.

Yayin da Malama Shatu daga karamar hukumar Lere ta bayyana yadda aikin gida ya sa maigida da babban dan sa suka mayar da ita matar su da kuma yadda ta fuskanci kyara daga uwargida.

Ita ma Maryam Adamu ta koka ne da yadda ta fuskanci kyara daga mahaifin ta da baya son ‘ya’ya mata duk da kasancewa ita kadai ce mace a tsakanin ‘ya’ya biyar a gidan su, wannan dalili ya sa ta bar gida ta shiga yawon duniya.

Daga karshe Kezia Iliya ta fadi irin cin zarafin da da fuskanta a wurin mahaifin ta da kishiyar mahaifiyar ta bayan kishiyar ta hana mahaifiyar ta zaman gidan ta kuma asirce mahaifin ta daga karshe dai ta gudu ta koma wurin kanin mahaifin ta.

Dukkan su sun jankalin al’umma dangane da illar cin zarafin ‘ya’ya mata sai suka bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su yi abinda ya dace.

Malaman addini ma ba a bar su a baya ba a bangaren bada gudumawa wajen yaki da cin zarafin mata.

Minister, Commissioner Unite to Empower GBV Survivors in Kano

Malam Abdulhayyu Musa Thabit Malamin addinin musulunci ne a jihar Kaduna ya ce musulunci tun fil’azal ya daraja ‘ya mace ya kuma kare mata mutunci. Malam ya ce addinance haramun ne cin zarafin ‘ya ce ta kowace hanya.

Shi ma a nasa bangaren Pastor Iliya Auta ya nuna yadda addinin kirista ya daraja ‘ya mace ya ce ko da Allah ya samar da Hauwa’u daga hakarkarin annabi Adamu yace masa ne ga abokiyar zama da zata taimaka masa ya samar masa amma ba baiwa ba, dan haka ya gargadi al’umma game da illar cin zarafin mace domin ita baiwar ALLAH ce kuma duk wanda ya ci zarafin ta ya sani ubangiji ya tanadar masa azaba mai tsanani.

Batun cin zarafin mata abu ne da ya sauya salo a yanzu da ake samun yawaitar sansanonin ‘yan gudun hijira sakamkon afkuwar wasu bala’o’I kamar su yakeyake da rikice-rikicen kansilanci da kuma ambaliyar ruwa wanda ake samun korafin cewa wasu lokuta Jami’an kungiyoyin bada agaji ko Jami’an tsaro dake ba sansanonin kariya ko ma wasu daga cikin samari ko maza a sansanonin suna latata da mata ‘yan mata ‘yan gudun hijiran bayan sun tilasta musu ko yi musu barazana.

Bridge Connect Africa Initiative Trains 50 GBV Survivors in Kano

Captain Abdullahi Bakoji mai ritaya shi ne shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa IHC reshen jihar Kaduna, ya ce hanyoyin magance matsalar cin zarafin mata shi ne yawaita tarukan wayar da kai da ilmantar da al’umma game da hakkin mata kamar yadda sashe na 1 da na 3 da kuma na 5 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar kan kare mutuncin dan Adam.

Yace na biyu shi ne kafa dokoki masu tsairi domin hukunta masu wannan mummunar dabi’a sai kuma samar wa mata jari ta yadda matasan da suka tsira daga cin zarafin su su samu su dawo cikin hayyacin su sai kuma sanya kungiyoyin addinai cikin duk wasu harkoki da gwamnati ke yi game da yaki da cin zarafin mata.

A nata bangaren shugabar kungiyar lauyoyi mata ta duniya reshen jihar Kano Barr. Bilkisu Ibrahim Sulaiman, a tattaunawar ta da manema labarai a ranar Laraba a wani bangare na makon yaki da cin zarafin mata ta duniya ta bayyana cewa cin zarafi ba wai ya tsaya ne kawai a fyade ba, wata matsala ce da kan dabaibaye iyali, dama al’umma baki daya.

Inda tace akan samu hakan a gidaje ko unguwanni ko makarantu ko wuraren aiki da sauransu.

Ta kuma bayyana illolin da hakan ke haifarwa da suka hada da hana yara mata damar samun nasara a rayuwa kamar sauran mutane. Ta ce a kokarin kungiyar na kawo sauyi suna kira ga al’umma su hada hannu da kungiyar domin dakile karuwar matsalar.

Kwamishinar kula da harkokin mata ta jihar Kaduna Hajiya Rabi Salisu ta bayyana irin kokarin da bangaren gwamnatin a matakai daban daban ke yi ne wajen yaki da dabi’ar cin zarafin mata ta ce gwamnati a shirye take ta yi amfani da duk wata doka da aka tanadar kan masu cin zarafin mata.

kwamishinar tace bisa wannan kokari da suke yi kwalliya na biyan kudin sabulu domin kuwa ana samun matukar saukin al’amarin, tace a bayabayan nan korafe-korafen da suke samu ya ragu a kan wanda ake samu shekarun baya kuma da yardan ALLAH za su ci gaba da zage damtse har sai sun kawo karshen matalar cin zarafin mata baki daya musaman a Najeriya.

KWAMISHINAR KULA DA HARKOKIN MATA TA JIHA KADUNA HAJIYA RABI SALISU

A karshen mutane sun Yaba tare da jinjina ma gwamnatin jihar Kaduna a kokarin da take Yi game da chi gaba da kwato yanchin mata da kananan Yara wadanda aka chi zarafin su tare da hukunta masu aikata laifin chin zarafi domin ya zama izina ga sauran mutane.

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version