Safiyanu Dantala Jobawa

Majalisar karamar hukumar Garun mallam a jihar Kano, ta ba mazauna kasuwar Kwanar Gafan wa’adin kwana bakwai da su tashi daga cikinta har zuwa wani lokaci nan gaba.

Shugaban K/H Garun Malam Ya Aike Da Sakon Kirsimeti

Shugaban karamar hukumar, Hon Barr Aminu Salisu Kadawa ne ya bada umarnin hakan a wajen bikin kaddamar da sake fasalin farfado da tattalin arzikin yankin.

Kadawa ya ce “Duba da irin yadda kasuwar aka mai da ita tamkar wata mafaka da cibiyar yada badala maimakon ainihin yin abun da aka kafa kasuwar tun farko.

Sai ga shi an buge da yin abubuwan da suka sha banban da manufar kasuwar.

Don haka ya bukaci tare da mazauna kasuwar da tattara kayansu su bar wajen, tun kafin ranar 1 ga watan Janairu 2025.

K/H Tarauni Ta Yi Alkawarin Aiki Da Kungiyoyin Cigaban Alumma

Ya ce “Duk wanda aka kama za a hukunta shi. Inda ya bayyan cewar nan gaba za a bayyana lokacin da za a yi bikin sake budeta don cigaba da kasuwancin iri daban-daban ba ma na kayan Gona ba har nau’in sauran ababan more rayuwa.

Daga karshe ya bukaci yankasuwa da zo don saka jarinsu a kasuwar.

Wani malamin addinin islama, Imam Abdullahi Yusif Chiromawa, ya yi jawabi akan yadda kasuwar Kwanar Gafan ke barazana ga tarbiyar yaransu, ya ce abun ba dadin ji balle gani.

Malam Abdullah ya ce “Kasuwar ta zama wajen aikata zinace-zinace ,Luwadi, da madigo ga matasa da kuma kawo matan aure.

Daga na kara da bayyana kasuwar mafakar Barayi da yanfashi da masu safarar mugagga kwayoyi. Imam Abdullahi, ya gode shugaban karamar hukumar bisa namijin kokarin da yanuna don kaucewa kara fadawa cikin fushi Allah.

Tun da a jawabinsa kwamishinan yansandan Kano, S.A Gusau kuma babban bako a wajen, ya ce

“tuni tunaninsu ya ke akan kasuwar Gafan yadda za su kawo karshen mazauna cikinta bayan karewar kayan noma na rani.

Amma lokaci ya yi da hukamar tsaro za ta sa’ido ta ga masu tsauri-Ido. Kuma nan take ya bada umarni daga ranar 25 ga watan Disamba 2024 kowa ya bar kasuwar.

A karshe taron sabunta kasuwar kwanar Gafan ya samu halartar manyan baki daban-daban wadan da suka hadar da jami’an tsaro, da wakilin bincike na jihar Kano Abdullahi(OCSID Kano) da hukumar kare yancin dan’adam(Human Right Network) da Sarkin Noman Kano Alh Yusif Nadabo Chiromawa da masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Garun mallam.

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version