Shugaban Karamar Hukumar Tarauni Ya Yi Alkawarin Yin Aiki Tare Da Kungiyoyin Ci Gaban Al’umma

Shugaban karamar hukumar Tarauni, Hon. Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya bayyana hakanne lokacin da kungiyoyin ci gaban al’umma a yankin suka kawo masa ziyara ofishinsa

Tarauni LGA Pledges Support for Community Development Groups

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Tarauni Adamu iliyasu Hotoro tafitar yace Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure Sekure yace ya daukin kudurin yin aiki tare da kungiyoyin don tabbatar da cewa kowane bangare na rayuwar jama’a yana samun tallafi.

Inda yakara da cewa Wannan zai taimaka wajen kawo cigaba a harkar ilimi, lafiya, tsaro, da sauran fannonin more rayuwa.”

Shugaban K/H Tarauni Ya Rantsar Da Kansiloli Masu Gafaka

Kingiyoyin da suka kawo ziyarar sun Hadar da kungiyar iyaye marayu na karkaksara, kungiyar Sekure media, kungiyar izala ta karamar hukumar Tarauni dakuma kungiyar Hawan Kara .

Shugaban ya kuma yi kira ga kungiyoyin da su ci gaba da bayar da hadin kai tare da kawo sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen bunkasa yankin.

Ahmed Ibrahim Muhammad sekure Yakuma tabbatar da cewa karamar hukumar Tarauni za ta samar da dukkan kayan aiki da goyon baya don tabbatar da nasarar wannan hadin gwiwa tsakanin karamar hukumar Tarauni da Alumma.

A jawabinsa tun da fari sakataran jami’iyar NNPP na karamar hukumar Tarauni Kuma Mai bayar da shawara kan harkokin siyasa Mallam Ali sani Zaki ya jaddada cewa shugaban karamar hukumar Tarauni kofarsa a za a bude take domin sauraron bukatun jama’a a kowanne lokacin.

Ya Kuna yi kira ga kingiyoyin dasu Kara Sanya shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure cikin addu’oi domin ya cigaban da Samun dama wajan kawo manyan aiyyukan raya kasa a fadin yankin Baki Daya.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version