A yau ne shugaban karamar hukumar Tarauni Alh Ahmed Ibrahim Muhammad sekure ya jagoranci bikin rantsar da sabbin kansilolin masu gafaka a fannoni daban daban a dakin taro na Majalisar kansilolin yankin dake sakatariyar karamar hukumar Tarauni

Shugaban karamar hukumar Ahmed Ibrahim Muhammad yace wannan Wani mataki ne nuna jajircewar shugabancin karamar hukumar domin cigaba da samar da sabbin shugabanni masu kishin da cigaban al’umma.

Ahmed Ibrahim Muhammad Sekure, ya bayyana cewa wannan rantsuwa na daga cikin kokarin gwamnatin sa na ganin an samu shugabanni nagari da zasu rika ba da shawara tare da gudanar da al’amuran gwamnati cikin gaskiya da amana. Inda Ya kara da cewa, wannan mataki zai kara wa karamar hukumar kwarin gwiwa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba a yankin.

Jami’in yada labarai na karamar hukumar Tarauni Wanda shine Mai magana da yawun shugaban karamar hukumar ya rawaitomana cewa an Rantsar da kansiloli riko da suka hadar Hajiya Husaina Muhammad kansilan PRS, Captain Abubakar Bello kansilan wesh,sani Bashir Ja’oiji kansilan ilimi, Amir Abdullahi kima kansilan lafiya, usman Suleman Adamu kansilan works,Umar Faruk Mubarak kansilan Agric,dakuma Isah Adamu Bashir kansilan community dakuma Safuwan Abdullahi Mikail Religious affairs and cheitency affairs

Sauran sun haɗar da masu bawa shugaban karamar hukumar shawara Aliyu sani Zaki Mai Bada shawara political,Sulaiman Musa Sulaiman Mai Bada shawara akan information and public Relation,Binta sani magaji Mai Bada shawara akan harkokin mata, Kabiru sani Mai Bada shawara akan jindadi da walwalar jama’a, Safuwan Suleman Mai Bada shawara akan ilimi, Nafiu Tashir Mai sharawa akan Albarkar katun kasa da ma’adanai,Yahaya wada Haruna harkokin matasa da wasanni,Auwal Mai wada Mai Bada shawara akan Agric,Umar Baba Dashiru Mai Bada shawara akan kasuwanci da zuba jari, Abubakar sani Hassan Dan Baris Mai Bada shawara akan Samar da Ruwan sha Hassan,

An gudanar da wannan rantsuwa cikin tsari da ladabi, tare da halartar manyan jami’an gwamnatin karamar hukumar da wakilan al’umma.

Majistry Hajiya Rakiya Tanko Itace ta Rantsar da sabbin kansilolin riko da masu bawa shugaban karamar hukumar shawara

Shugaban jami’iyar NNPP na karamar hukumar Tarauni Alh Inuwa Suleman Hugan da Daraktan Mulki na yankin Alh Abdulkadir muhammad Arabu da ma’ajjin karamar hukumar Alh Bello Hassan dakuma Shugaban sassa Suleman Umar sunyi fatan cewa sabbin shugabannin za su ba da gudunmuwa mai inganci wajen ci gaban al’umma da tabbatar da zaman lafiya da walwala a yankin.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version