Kungiyar WOFAN ta jaddada kudirinta na cigaba da horar da ma’aikatan ta a fannoni da dama domin bunkasa aikin kungiyar.

Kungiyar ta ce bada horo ga ma’aikatan na daya daga cikin abubuwan da ta bawa mahimmanci don ganin an kara inganta kwarewar su ta yadda aiyukan kungiyar zasu kara inganta

Daraktar kungiyar ta WOFAN-ICON2, Dakta Salamatu Garba ce ta bayyana hakan a yayin wani horo na kwanaki biyu ga ma’aikatan WOFAN da ta shirya, kan daukar hoto, bidiyo da kuma amfani da na’urar daukar hoto mai tashi sama da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Dokta Garba ta ce an horas da ma’aikatan ne domin a kara ilimin su kan yadda ake daukar hotuna masu inganci, da kuma amfani da na’urar daukar hoto mai tashi sama ta yadda za suyi amfani da ita su dauko guraren da zasuyi wahalar zuwa da kafa

“Mun horar da ma’aikatan mu kan amfani da na’urar daukar hoto mai tashi sama domin inganta ayyukanmu, koda an sami ambaliyar ruwa Allah ya kiyaye, zamu iya amfani da wannan na’ura domin daukar hoto ko bidiyo na gurin da abin ya faru, hakan zai taimaka mana domin gano asarar da ambaliyar ta haifar da kuma abubuwan da suka lalace, ko kuma idon muna buƙatar auna girman gonaki, na’urar zata taimaka sosai wajan aiwatar da aiyukan cikin sauki.”

‘’Shi ya sa muka dauko ma’aikatanmu daga akasarin jihohin da muke gudanar da aiyukan mu kamar Kano, Bauchi, Gombe da kuma babban birnin tarayya Abuja domin a basu horo.

A cewarta, tallafin da WOFAN ke samu daga gidauniyar Mastercard mai taken WOFAN-ICON2 da nufin rage radadin talauci a Afirka daga shekarar 2020 zuwa 2030 da miliyan 10 a Najeriya, WOFAN na yin wannan kokarin ne ta hanyar tabbatar da cewa sama da mutane 600,000 masu rauni musamman mata da matasa sun sami rayuwa mai kyau.

“Taimakon Gidauniyar Mastercard ga WOFAN don kawar da talauci ya kasance na tsawon shekaru 5 inda za mu samar da rayuwa mai kyau ga mata da matasa sama da 600,000, duk da haka, sai kuma Allah yasa aka ƙara mana tsayin shirin da wasu shekaru 5 din, wanda a halin yanzu muna aiki don tallafawa mutane sama da miliyan 1.3 masu rauni don taimakawa rayuwar su.

’Don haka wannan horon da mukaiwa ma’aikatanmu na daga cikin shirin domin mun mayar da hankali ne kan raya karkara da tallafa wa manoma, mata da kuma matasa. Muna bukatar mu nuna musu labaran nasarorin da muke samu da kuma ƙalubalen da ake fuskanta.’

“A yanzu haka, muna aiki da manoma sama da 20,000 a yankunan karkarar a Abuja, muna aiki a Kano, Jigawa, Bauchi, Gombe da Adamawa da sauransu.”

SolaceBase ta rahoto cewa mai koyar da Ɗaukar hoton, Malam Abdulwahab Sa’id Ahmad ya horas da ma’aikatan hanyoyin da ake ɗaukan hotuna masu inganci tare da ma’auni da lissafin lokacin daukar hoto.

Har ila yau, wanda ya horar da ma’aikatan kan na’urar daukar hoto mai tashi sama Malam Abdulaziz Abdulaziz, ya bukaci su da su cigaba da gwada amfani da ita domin samun kwarewa sosai.

SOLACE BASE HAUSA

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version