Hukumar tace fina-finai da Dab’I ta Jahar tayi mamakin jawabin Dauda Kahutu Rarara dake cewa babu wata kotu da take neman shi a ta bakin wani da wata kafar yada labarai a Kano ta saka muryarsa da sunan yana magana da yawun mawakin.

Tun a ranar 8/11/2024 kotun mai lamba 47 dake unguwar No-man’s-land a jahar Kano ta aikawa da mawakin takardar sammaci a ofishinsa dake kan titin gidan zoo a Kano kuma bayan rashi samun shi kotun ta kara tura mishi da sakon karta kwana ta hanyar Tex message tare da manhajar whatApp inda aka bukaci ya bayyana a gaban kotun a ranar 13/11/2024.

Dangane da maganar da wakilin mawakin yayi na cewa ba’a a Kano mawakin yayi wakar ba hakan ya tabbatar da cewa mawakin ya kwana da sanin laifin da Hukumar take zargin ya aikata.

Haka kuma, yana da kyau al’umma su kara fahimtar cewa matsawar dan film, marubuci ko mawaki ya taba yin rijista da Hukumar to dole ne ya bi dokokin Hukumar a duk inda yake kamar yadda ya dauki alkawari a yayin da zai cike form.

Bugu da Kari Hukumar nada hurumi na saka ido, bada shawara ko hukunta duk wani aiki daya shafi aiyukan da suka rataya a kanta matsawar ya shigo Jahar Kano ko a ina akayi aikin.

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version