Dakarun Rasha sun kama sojan Ukraine Oleksandr Matsievsky a shekarar farko da aka kaddamar da yaƙi.

Daga baya wani bidiyo ya bayyana da ke nuna shi yana shan taba a daji, kila kusa da ƙabarin da aka tilasta ma shi haƙawa.

“Nasara ga Ukraine!” ya faɗa wa waɗanda suka kama shi. Daga baya aka ji ƙarar harbi ya faɗi ya mutu.

Gaza Conflict : Over 42,000 Palestinians Killed, 97,720 Wounded

Bayan kisan shi akwai wasu da dama.

A watan Oktoban wannan shekarar, an bayar da rahoton kashe sojojin Ukraine shida da sojojin Rasha suka kama a lardin Kursk.

Talla

Masu gabatar da ƙara na Ukraine na bincike kan lamarin haɗi da hoton da ke nuna hotunan gawarwakinsu.

“Na gane shi daga ganin wandonsa,” kamar yadda mahaifiyarsa ta shaida wa wata kafar yaɗa labarai Suspilne Chernihiv.

“Ni saya masa lokacin da zai yi tafiya zuwa bakin teku. Na kuma san an harbi kafaɗar shi. Za ku iya gani a hoton.”

Jerin mutanen da aka kashe na da yawa. Masu shigar da ƙara na Ukraine na gudanar da bincike kan rahoton fille kan mutane da kuma amfani da takobi wajen kisan sojan Ukraine da aka ɗaure hannunsa a baya.

A wani bidiyon, an ga wani matasan sojojin Ukraine 16 an jera su aka buɗa masu wuta.

Dakarun Rasha sun ɗauki hotunan yadda aka kashe sojojin, yayin da kuma wasu jirage marar matuka na Ukraine ne suka ɗauka daga sama.

Turereniyar Karbar Abinci A Coci Ta Yi Sanadiyar Rayukan Mutane 10 A Abuja

Ana gudanar da kisan ne galibi a wani fili da ba za a iya tantancewa ba, wanda zai bayar da wahalar gano asalin inda suke.

Amma masu bincike na BBC sun yi ƙoƙarin tabbatarwa – kamar yadda aka fille kan wani – kuma yana sanye da kakin soji na Ukraine kuma bidiyon bai daɗe ba.

Yawan kisan na ƙaruwa

Masu shigar da ƙara na Ukraine sun ce aƙalla fursunonin yaƙi na Ukraine 147 dakarun Rasha suka kashe tun ƙaddamar da mamayar ƙasar. 127 a wannan shekarar.

“Yawan kisan a bayyane yake,” in shi Yuri Belousov, shugaban ɓangaren da ke kula da yaƙi na masu gabatar da ƙara na Ukraine.

“Ana gudanar da kisan a tsare daga watan Nuwamban wannan shekarar kuma an ci gaba. Abin takaici yana ƙaruwa musamman a bazara.”

Dokar ƙasa da ƙasa – musamman yarjejeniyar Geneva – ta yi tanadi kariya ga fursunonin yaƙi, kuma kisan aikata laifin yaƙi ne.

Rachel Denber, mataimakiyar Daraktan ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Human Rights Watch a Turai da tsakiyar Asiya ya ce babu ƙarancin hujjoji kan zargin cewa sojojin Rasha na kisan fursunonin Ukraine. Rashin zartar da hukunci ta taka rawa, kuma dakarun Rasha na da mamyan tambayoyi da za su amsa.

“Wani umarni ne wannan ɓangaren yake da shi, ko dai a hukumance daga kwamandojinsu? Ko kwamandojin suna da cikakkiyar masaniya game da abin da yarjejeniyar Geneva ta ce kan kula da fursunonin yaƙi?

Me kwamandojin rundunar sojin Rasha ke fada wa ɓangarorinsu game da ayyukansu? Waɗanne matakai ne ake bi na binciken irin wannan yanayin?”

Zuwa yanzu babu wani abin da ke nuna Rasha na gudanar da bincike kan zargin sojojin ƙasar na kisan fursunonin Ukraine.

A cewar Vladimir Putin, dakarun Rasha na kula da fursunonin Ukraine bisa kiyaye dokoki na ƙasa da ƙasa.

Ana kuma zargin dakarun Ukraine da kisan fursunonin yaƙi na Rasha, amma yawan zarge-zargen ba su da yawa.

Yuri Belousov ya ce ɓangaren masu shigar da ƙara na Ukraine sun ɗauki irin zarge-zargen da muhimmanci kuma suna gudanar da bincike. Amma zuwa yanzu babu wanda aka hukunta.

Kungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Human Rights Watch ta ce tun ƙaddamar da mamayar Ukraine a watan Fabrairu, dakarun Rasha sun “aikata laifuka ciki har na laifukan yaƙi da ya kamata a gudanar da bincike. “

BBC HAUSA

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version