Liverpool da alama za ta jingine zawarcin ɗan wasan Brighton da Brazil, Joao Pedro har zuwa lokacin bazara saboda alamomin da ƙungiyarsa ke nunawa na da wuya ta sayar da matashin mai shkara 23 a kasuwar watan Janairu. (Football Insider)
Corruption Hinders Sports Growth in Nigeria-Gara Gombe
Paris St-Germain ta shirya biyan yuro miliyan 100 kan ɗan wasan Newcastle United da Swedeen Alexander Isak, mai shekara 25. (Fichajes.net – in Spanish, external)
Ƙungiyar PSG ta Faransa na shirin biyan yuro miliyan 58 kan ɗan wasan Athletic Bilbao Nico Williams – amma Manchester United da Barcelona kowa ya nuna kwaɗayinsa kan matashin mai shekara 22. (El Desmarque – in Spanish, external)
Barcelona ta fid da rai kan ɗan wasan Netherlands Frenkie de Jong kuma da alama ɗan wasan na tsakiya da wuya ya bar Sifaniya. (Relevo – in Spanish)
Leicester City za ta gabatar da yarjejeniyar fam miliyan takwas kan ɗan wasan Argentine, Valentin Gomez mai shekara 21 daga Velez Sarsfield. (Sun)
Madobi Council Chairman Distributes Sports Kits to Football Clubs
Newcastle na cikin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan Barcelona, Eric Garcia, mai shekara 23, amma tsohon ɗan wasan na Manchester City na son ci gaba da zama a Nou Camp. (Sport – in Spanish)
Crystal Palace na son sayen ɗan wasan Benfica da Jamus Jan-Niklas Beste, mai shekara 25 a watan Janairu. (Sky Sports Switzerland)
Real Madrid na duba yiwuwar sayen ɗan wasan Sifaniya mai shekara 22 Rafa Marin, da ke samun horo a makarantar kwallo ta matasa da kuma taka leda yanzu haka a Napoli. (Fichajes.net – in Spanish)
Blackburn Rovers da Burnley na son sayen tsohon ɗan wasan Sheffield United, Oli McBurnie mai shekara 28 daga Las Palmas. (Sun)
Ɗan wasan gefe a Sifaniya Lamine Yamal mai shekara 17 na gab da tsawaita zamansa a Barcelona zuwa 2030. (Nicolo Schira)
Newcastle za ta bai wa ɗan wasan Ingila Callum Wilson, mai shekara 32, daman barin ƙungiyar a karshen kwantiraginsa na wannan kaka. (Football Insider)
BBC