Fim din sa mai suna Lagaan da aka shirya a kan wasan kricket (Cricket) a karni na 19 lokacin mulkin Birtaniya, na daga cikin wadanda a ka zaba domin samun lambar yabo a rukunin fim din da ya fi fice da ba na turanci ba a shekarar 2002.
A yanzu kuma Khan na kokarin kafa tarihi da fim din Laapataa Ladies. Idan ya yi nasara, fim din zai kasance fim din Indiya na farko da ya samu lambar yabon mai matukar muhimmanci.
Dan Ibro: A True Icon in the Nigerian Entertainment Industry
A ranar Talata ne zai tabbatar ko fim din ya samu shiga jerin finafinan da ke neman lambar yabon.
Khan ya ce bai san wani irin muhimmanci zai bai wa samun lambar yabo ba. “Masana’antar finafinai na cike da son rai” a cewarsa.
Sai dai ya yarda cewa samun lambar yabon zai kasance abu mai muhimmanci ga Indiya.
“A gani na yan Indiya na matukar son fim kuma mun dade muna so mu samu lambar yabo a fim din Indiya a Oscars, wanda har yanzu ba mu samu nasara ba. A don haka yan kasar za su yi farin ciki mara misaltuwa idan muka yi nasara” inji shi.
“Saboda yan kasar da kuma kasarmu, zan yi farin ciki sosai idan muka samu lambar yabon.”
Fim din “Laapataa Ladies” wanda aka yi shi a kauye, yana ba da labarin wani matashi da ya yi kuskuren kai amaryar da ba tasa ba gida. A gefe guda kuwa matarsa ta bace, ta ƙare ita ke kula da kanta.”
Fim din na barkwanci ne da ke nuna abubuwan da ake yi wa mata, kuma ya tabo batun nan mai jan hankali na cin zarafin mata a gidaje.
Kano Censors Board NBC Partner To Ban Unlicensed Films Books
Khan ya ce fim din na nuna abubuwa ma su muhimmanci a kan matsalolin mata, yancin su, da kuma hakkin su na zaben ma kansu abunda su ke so su yi”.
Ya bayyana cewa tun da farko wadannan batutuwan ne ma suka janyo hankalin sa ga fim din.
“ A wasu lokutan kana samun dama a matsayinka na mai ƙirƙire ƙirƙire domin ka wayar wa mutane kai kan wasu matsaloli da ake fuskanta a cikin alumma, “ inji shi.
“ Mata a fadin duniya na fuskantar kalubale da dama a rayuwarsu. Mata na fuskanta matsaloli. Saboda haka na ji cewa ga wani labari nan wanda ya fito da hakan a yanayi mai kyau, shiyasa na so in shirya shi.”
Kiran Rao da Aamir Khan sun halarci tantance Fim din Laapataa Ladies a ranar 27 ga watan Fabrairun 2024
Khan ya kuma bukaci cewa tsohuwar matar sa Kiran Rao ce zata bayar da umurnin fim din.
Aamir da Kiran wadanda suka yi aure a 2005, sun sanar da rabuwar su a shekarar 2021. Amma sun kasance tare, a aiki da kuma lokutan da ba na aiki ba.
“ Ina tunanin dalilin da ya sa na zabi Kiran shi ne, na san cewa za tayi aikin cikin gaskiya, kuma abun da na so kenan,” inji shi.
“ Abubuwan mu sunzo daya sosai. Muna son junan mu sosai, mu na mutunta juna.
“ Alaƙar mu ta dan sauya- amma hakan ba ya nufin abunda mu ke ji kan junan mu ya ragu ba ko wani abu makamancin haka.”
Sai dai kuma ba wai hakan na nufin komai na tafiya ba gargada bane.
Khan ya ce su na dan samun gardama a wurin shirya fina-finai.
“ Ba ma iya shirya fim ba tare da munyi gardama ba. A kowani mataki muna gardama kuma duk mu na da ra’ayi mai karfi,” a cewar shi.
‘’ Sai dai kuma ba ma daukan abu da zafi. Kawai mu na kokarin shawo kan ɗaya a cikin mu ne kan hanyan da ya fi dacewa a yi wani abu.’’
BBC HAUSA