Iran ta ɗage haramcin da ta ƙaƙaba kan manhajar sada zumunci ta Whatsapp.

Kamfanin dillancin labarai na ƙasar ya ce wata hukuma ta kaɗa ƙuri’ar cire duk takunkuman da aka ƙaƙaba kan Whatsapp da rumbin sauke manhajoji na Google Play na tsawon fiye da shekara biyu.

Amir Khan Zai Kafa Tarihi Da Fim Din Sa Na Laapataa Ladies

Tsarin sirranta bayanai na manhajar ya sa ya yi wuya ga hukumomin ƙasar su bibiyi hirarrakin mutane kuma hakan ya ci karo da dokokin amfani da intanet masu tsauri da ƙasar ta kafa.

Morocco Za Ta Ba Mata Ikon Hana Mazajen Su Kara Aure

Amfani da Whatsapp a Iran ya zama jidali saboda da wuya saƙonnin da aka tura ta manhajar su isa ga wanda aka aikawa.

BBC HAUSA

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version