A jiya Laraba ne Arsenal ta bi Brentford har gida ta zura mata ƙwallo uku, yayin da Brentford ɗin ta zura ɗaya.

Wannan nasara ta sa Arsenal ta koma matsayi na biyu a kan teburin gasar Premier, inda take ƙasan Liverpool da tazarar maki shidda.

Labaran Wasannin Kungiyoyin Kwallon Kafa A Nahiyar Turai

A lokacin da Bukayo Saka ya ɗingisa zuwa wajen fili tun kafin hutun rabin lokaci a wasan Arsenal da Crystal Palace, ranar 24 ga watan Disamba, an shiga taraddadi game da yadda Arsenal ɗin za ta iya cin ƙwallaye ba tare da Saka ba.

Saka, mai shekara 23 da haihuwa ya kasance jigo a ɓangaren zura ƙwallayen Arsenal, inda ya ci biyar sannan ya taimaka aka zura 10 a wasannin Premier 16 na farkon wannan kakar wasanni.

Kungiyar Juventus Ta Yi Watsi Da Zawarcin Marcus Rashford

To amma, wasu ƴan wasan ƙungiyar su ma sun yunƙuro. Kai Havertz, Gabriel Martinelli, Gabriel Jesus, Declan Rice da Mikel Merino duk sun samu nasarar zura ƙwallo bayan raunin da Saka ya yi.

Hakan kuma ya sanya matashi Ethan Nwaneri shi ma ya fara haskawa – inda aka fara da shi a wasan da Arsenal ta kara da Brentford

BBC HAUSA

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version