Mai Girma Kwamishiniyar Ma’aikatar Harkokin Mata, Yara da Masu Bukata ta Musamman, Hajiya Aisha Lawan Saji Rano, ta aiyana Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a matsayin uba na hakika ga marayun Gidan Yara na Nassarawa.

Kwamishiniyar ta yi wannan ikirarin ne jim kadan bayan da ya yi wa daya daga cikin marayun waliccin daurin auranta jiya Jumu’a bayan da ta yi nasarar samun mijin aure.

Mai Girma Saji ta ce gwamnan wanda ya samu wakilcin Kwamishinan Harkokin Addini ya tabbatar wa da duniya shi uban marayu ne, wanda ke tare da su , yana nuna musu gata da kusancin da duk mai uba ke samu.

Ta kara da cewa, gatan ba a walicci kawai ya tsaya ba, “Gwamna Yusuf ya yi wa amarya gatan da ba duk mai uba zai samu irinsa ba. Ya yi mata kayan daki na fada, har da firinji, talabishan, garar kayan abinci da sauran su. Sannan an yi mata walima ta doka misali a event center.

“Allah ya saka wa Mai Girma Gwamnan da mafi girman alkhairinSa a bisa wannan kyautatawa da ya yi wa wannan amarya tamu”, in ji Hajiya Saji.

Tun da farko ta ce Gwamnan da kansa ne ma ya gayyaci al-ummah wajen daurin auren a katin gayyatar, gatan da ta ce ba lalle ba ne su a matsayin su na kwamishinoni su samu irinsa.

Ita ma Kwamishiniyar wacce take a matsayin uwa ga marayun ta tura wakilci na manyan daractocin ta maza da PA nata a yayin daurin aurtan da aka gudanar a massacin Jumu’a na Al-Furqan, kuma ya samu halartar dunbum masallata.

An dauran auran a bisa sadaki dubu dari (#100,000) wanda aka biya lakadan.

Tun da fari, amaryar Rabi Muhd Sani wacce daya ce daga cikin yaran gidan Nassarawa Children’s Home, ta samu mijin aure Nasiru Musa wanda ya bi hanyoyin da suka dace na neman aure ta hannun Kwamishiniya Hajiya Saji.

Mai Girma Saji wacce ke cike da farin ciki yayin wannan biki ta kasance tare da daractocin ta mata da sauran ma’aikatan gidan marayun na Nassarawa.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version