Majalisar dokokin jihar kano ta nuna rashin Jin dadinnta ga aikin kwangilar gyaran Asibitin Nassarawa bisa Rashin gamsuwa da kayan da ake amfani da su aikin.

Shugaban kwamitin majalisar mai kula da ayyuka Alhaji Yusuf Bello Aliyu ne ya bayyana hakan ziyarar Duba aikin Asibitin , wanda yace matsayin kayan da Dan kwangilar ke amfani da su a gyaran Basu aka sahale ba kamar yadda Suka ganewa idanun su.

Kwamitin ya kuma bayyana damuwar sa bisa yadda aikin gyaran ofishin mataimakin Gwamna da Gidan sa, ke Jan kafa, dukkuwa da watannin da Dan kwangilar yayi yana aikin, wanda yace akwai matsala ace mataimakin Gwamna yana kwana da kuma gudanar da aiki a inda ba nanne aka tanadar masa ba.

Majalisar ta kuma gayyaci dan kwangilar daya ya bayyana gaban kwamitin majalisar don amsa tambayoyi.

Hakazalika kwamitin ya Kai makamanciyar wancan ziyara izuwa maaikatar kimiyya da fasaha ta kano da hukumar raya al’adu ta jihar Kano

Share.
Leave A Reply

Exit mobile version