Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa mata masu zaman kan su, da ake kira “runs girls,” za su rika biyan haraji daga abin da suke samu a ƙarƙashin sabon tsarin haraji na ƙasa.
Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Tsare-tsaren Haraji da Gyaran Haraji, Mista Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin wani taron tattaunawa a Cocin Redeemed Christian Church of God, City of David, Lagos.
Protest: Kano Commercial Sex Workers Decry Low Patronage
A cewar Oyedele, sabon tsarin ba ya bambance tsakanin halastaccen kuɗi da kuma wanda ba shi da halacci, illa kawai ya na duba ko mutum na samun kuɗi.
“Idan wata tana yin runs (aikin karuwanci), tana fita tana neman maza dole sai ta biya haraji a kai,”
Ya kara da cewa dokar na buƙatar kowa ya bayyana kuɗin da ya samu daga ba da sabis ko kaya, domin biyan haraji.
Sai dai ya yi karin haske cewa kuɗin kyauta ko na tallafi da ba a ba da shi saboda an yi wani aiki ko sabis ba, ba za a saka masa haraji ba.
“Idan kuɗin da ake tura musu kyauta ce, ba saboda sun yi wani abu ba, to wannan kyauta ce. Muna kiransa mu’amala ba ta musaya ba. Wannan ba shi da haraji,” in ji shi.
HPV Vaccine Community Outreach Records Encouraging Turnout in Kano
Wannan sauyi na faruwa ne bisa sabbin dokoki da suka haɗa da Dokar Haraji ta Najeriya, Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya, Dokar Kafa Hukumar Haraji ta Najeriya, da kuma Dokar Kafa Hukumar Haɗin Kai ta Haraji.

