Shugaban Majalisar Malamai ta jihar Kano Sheikh Malam Ibrahim Khaleel, yace ya kamata al’ummar musulmi su kara zage dantse wajen samar da hanyoyin da zasu kyautatawa marasa karfi dan ganin an samu Al’umma ta gari.
Malam Khaleel, ya bayyana hakane a wani taron Maulidi da aka gudanar a Kano wanda Mahmud Sa’id ADhahama ke gudanarwa ako wace Shekara a harabar gidansa dake Nasarawa GRA kano.
Kano Speaker Falgore Felicitates Muslims on Eid-Maulud
Da yake bayyana kyautatawa a matsayin halayen Manzo (S.A.W), Malam Khaleel ya ce, kyautatawar na daya daga cikin hanyoyin dake yaye talauci, inda ya kuma yabawa masu shirya tarukan da ake ambaton Manzon Allah irin hakan.
” Ya kamata wajen maulid Annabi S A W ya zamo a nutse saboda ana ambato Allah subhanahu wata’ala da Manzon Allah, rashin yin haka bai dance kuma kuma rashin girmamawa ne ga maulidin”.
Da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron Maulidin kan makasudin shirya taron, Mahmud Adahama yace, wannan taron ya zama na musamman la’akari da yadda Manzon Allah ( S.A.W) ya cika shekara dubu daya da fari Biyar 1500 da haihuwa dai-dai.
“Mun shirya Wannan Mauludin ne saboda soyayyar da muke yiwa Annabi Sallallahu alaihi wasallam, sannan kuma Mauludin na bana ya zo mana a wani Sabon Salo saboda a Wannan Shekarar ne aka cika shekaru 1,500 da haihuwar fiyayyen halitta Annabin Muhammad Tsira da amincin Allah su kara tabbatar a gare shi”. Inji Muhmoud
Maulud-Kano Deputy Gov Urges Muslims to Embrace Unity, Love
A karshe Mahmud Adahama, ya bukaci masu hannu da shuni da su rika tallafawa Al’umma musammanma marasa karfi. Domin samun saukin rayuwa Na Yau DA kullm.
An rufe taron wanda ya samu halartar Manyan mutane na ciki da wajen kasar nan, da Addu’a tare da fatan samun zaman lafiya a jihar Kano dama kasa baki daya.

